Ali Nuhu

Dan wasan Kuma mai bada umarnin a Shirin wasan ƙwaiƙwayo, an haife shi a shekarata 1974
Mukala mai kyau

ALI NUHU MUHAMAD

Ali Nuhu
Rayuwa
Cikakken sunaAli Nuhu Mohammed
HaihuwaMaiduguri, 15 ga Maris, 1974 (50 shekaru)
ƙasaNajeriya
MazauniKano
Harshen uwaHausa
Harshen Waja
Karatu
MakarantaJami'ar Jos
Matakin karatuDigiri
Bachelor of Arts (en) Fassara
HarsunaTuranci
Hausa
Larabci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'aJarumi, darakta, mai tsara fim da marubin wasannin kwaykwayo
Kyaututtuka
Imani
AddiniMusulunci
IMDbnm2683171
alinuhu.net
Ali Nuhu
Snapped with the greatest of all time Nigerian movie industry.jpg

An haifi Ali Nuhu a ranar 15 ga watan March a shekarar 1974 a Maiduguri, Jihar Borno, ya girma a jihar Kano, iyayen sa kuma ƴan Balanga ne a jihar Gombe dake arewacin Nigeriya.

Ali Nuhu ba bahaushe kamar yanda wasu ke fada ya fito daga kabilar "WAJA". cikakken sunan mahaifinsa shine "NUHU EMANUEL POLOMA"

Ali ya girma a hannun mahaifiyar sa a jihar Kano bayan sun rabu da mahaifinsa sakamakon bambancin addini, mahaifiyar sa ta rasu a shekarar 1999 shi kuma mahaifinsa ya rasu a shekarar 2020, a halin yanzu Ali Nuhu yana bin addinin Musulunci kamar mahaifiyar sa.

Ali Nuhu jarumi ne, marubuci, mai bada umarni kuma furodusa a masanatar shirya finafinai ta kannywood da Nollywood. Sannan kuma yakan yi rawa a wasu fina-finai.

Ali Nuhu yana finafinan sa cikin harshen Hausa da turanci, sannan kuma yana cikin manyan jarumai da suka kafa masana'antar shirya finafinai ta kannywood.


Shekarun sa 49, ya kuma karanci geography a jami'ar Jos wato "University of Jos" a turance.

Mutane suna masa inkiya da "sarki Ali Nuhu/ King of kannywood, wanda a ƙalla zuwa yanzu ya fito a finafina sama da 500+ wanda ya samu lambobin yabo da dama. ko a wannan shekara saida ya samu lambar yabon "best actor award in the Nollywood Europe Golden Award (NEGA 2023)".

Ya fara harkar finafinai tun a shekarar 1999 wato shekarar da mahaifiyar sa ta rasu da wani fim mai taken "ABIN SIRRI NE" ya kuma fito a finafinan masana'antar shirya finafinai ta kudancin Nigeria NOLLYWOOD irin su Tout too, The Ghost, The Millions and Diamonds in the Sky, da dai sauransu.

Jarumin yana da aure mata daya da yara biyu Ahmad da fatima

Alh Abdoul Embesey ii

Farkon rayuwa

An haifi Ali Nuhu Muhammad a Maiduguri, jihar Borno, a arewa maso gabashin Najeriya. Mahaifinsa Nuhu Poloma daga Balanga gari Jihar Gombe da mahaifiyarsa, da Fatima Karderam Digema daga Bama gidan gwamnatin jihar Borno. Ya girma a Jos da Kano.[1]

Aure

ali nuhu yanada mata daya da Yara guda biyu Ahmad Ali nuhu da Fatima Ali nuhu.

Ilimi

Ali ya yi karatu a Jami'ar Jos, Bayan karatun sakandare, ya sami digiri na farko a fannin ilimin na fasaha daga Jami'ar Jos. Yayi bautar kasa a Ibadan da ke jihar Oyo. Daga baya ya halarci Jami'ar Kudancin Kalifoniya don yayi kwas a fagen shirya fina-finai da fasahar sinima.[2]

Sana'ar fim

Ali Nuhu ya fara fitowa a fim ne a shekarar ta 1999 mai suna “Abin sirri ne”. An fi saninsa da rawar da yake takawa a "Sangaya" wanda ya zama dayan finafinan Hausa da suka fi samun kudi a lokacin. Ali Nuhu ya fito a fina-finai da dama, wadanda suka hada da Azal, Jarumin Maza, da Stinda a matsayin fitaccen Jarumi a wajen bayar da gudummuwa a yayin bikin bayar da kyaututtuka na African Movie Academy a (2007). A shekarar ta 2019, Ali Nuhu ya yi bikin cikarsa shekaru 20 a masana'antar nishadantarwa. Ya fito a fina-finai kusan dari biyar (500).[3]


Mabiya

inda akayi ittifaki akan yana da mabiya a Twitter sama da 140,000 da kuma mabiya a Facebook sama da 3,000,000 da kuma wasu a shafin Instagram sama da milyan 1,000,000.[4][5]

Fina finai a Kannywood

(BT) na nufin Ba Tabbas, ma'ana babu tabbacin kwanan wata da shekarar da fim din ya fita. Yayin da akwai wasu kuma da ake da tabbacin kwanan watan fitar su.

Fim↑ ShekaraFimShekara
AbayaBTAlhiniBT
Abin Sirri Ne1998AliBT
AlhiniBTAlkebbaBT
AliBT
AlkebbaBT
AmbatoBT
Aska TaraBT
Zuwa Da KaiBT
Uwar MijiBT
'Ya 'Ya NaBT
Ina Miji Na?BT
GambizaBT
Namijin DuniyaBT
Dama da HauniBT
Ga Fili Ga Mai DokiBT
Masu AjiBT
Zo Mu ZaunaBT
Mashi2003
Gida da WajeBT
YanayiBT
Farin WataBT
Sakayya1998
Harafin SoBT
Zuciya Ko RuhiBT
Sangaya2000
JIGAL2002
Bashin GabaBT
Mai Gadon ZinareBT
Ragowar YakiBT
Kishin MataBT
JurwayeBT
Fitilar DareBT
Rana da WataBT
Umarnin UwaBT
Gadan GaBT
Sabon ShafiBT
Hawan GirmaBT
KhalidBT
MaraichiBT
Har AbadaBT
QiyasiBT
ShamsiyyaBT
TawakkaliBT
RaliyaBT
Maryam DiyanaBT
RawaniBT
Ban Ga Masoyi BaBT
Gidan IkoBT
ZambaBT
KamilallaBT
NazariBT
Garinmu da Zafi (Dawo-Dawo)BT
BilalBT
MujadalaBT
BahaushiyaBT
Rariya2017
Dangin Miji2017
Ba Tabbas2017
Mansoor2017
Zuciya Da Hawaye2017
Wacece Sarauniya?2017
Jarumta2016
Mu'amalat2016
Dattijo2016
Shinaz2016
Igiyar Zato2016
Halacci2015
'Yar Tasha2015
Wutar Gaba2015
Bani Bake2015
Gamu Nan Dai2015
Uba da 'Da2015
Baya da Kura2015
Ba'asi2015
Sallamar So2015
Kurman Allo2015
Nasibi2015
Hanyar Kano2014
Sirrin Da Ke Raina2014
Mai Dalilin Aure (Match Maker)2014
Jinin Jiki Na2014
Garbati2014
'Ya daga Allah2014
Idan Hakane2014
Kanin Miji2014
Mati da Lado2014
Sai a Lahira2014
Munafikin Mata2014
Duniyar Nan2014
So Aljannar Duniya2014
Hujja2014
Hakkin Miji2014
Andamali2013
Dakin Amarya2013
Nadawo Gareki2013
Wani Gari2013
Da Kishiyar Gida2013
Haske2013
Lamiraj2013
Jarumin Maza2013
Fari Da Baki2013
Zuri'a2013
Mai Jego2013
Mai Farin Jini2013
Halisa2013
Matar Jami'a2013
Kudi A Duhu2013
Madubin Dubawa2012
Gani Gaka2012
Wani Hanin2012
Kudi A Duhu2012
Son Zuciya2012
Dan Marayan Zaki2012
Kara da Kiyashi2012
Rai Dai2012
Hubbi2012
Bazan Barki Ba2012
Son Mai So2012
Blood and Henna2012
Maza Da Mata2012
Noor (The Light)2012
Talatu2012
Kona Gari2012
Adamsy2011
Alhaki Kwikwiyo2011
Armala2011
Malika2011
Tsaraba2011
Mutallab2011
Mai Zamani2011
Jaraba2011
Ke Duniya2011
Toron Giwa2011
Fisabilillahi2011
Muradi2011
Rai Da Buri2011
Ankwa2011
'Yan Mata2010
Mai Ladabi2010
Sarauta2010
Kukan Zaki (the Lion’s Cry)2010
Balaraba2010
Ladidin Baba2010
Dan Sarki2010
Sai Wata Rana2010
Wasila2010
Artabu (A Mazauna)2009
Dijangala2008
Hafsah2007
Bana Bakwai2007
Sabon Sarki2006
Jamhuriya2005
Taurari2005
Gwamnati2003
zero hour2020

Bada umarni

ShekaraSunaMatsayiSaloKamfanin daya shirya
2007SitandaJarumiWasa
2011Carbin KwaiJarumiWasa
2012Madubin DubawaJarumiWasa
2012Last Flight to AbujaJarumiWasaNollywood Film Factory
2013Blood and HennaJarumiWasaNewage Networks
2013Confusion Na WaJarumiWasCinema KpataKpata
2013Wani HaninJarumiWasa
2014Matan GidaJarumiWasa
2015Jinin JikinaJarumiWasa
2016NasibiJarumiWasa
2016OjukokoroJarumiWasaSingularity Media
2017Banana Island GhostJarumiWasa

Lamban girma

Ali Nuhu yana daga cikin jaruman fina-finan Hausa wadanda ke gaba-gaba wajen samun gagarumar nasarori a masana'antar ta Kannywood dama ta mutanen kudancin Najeriya wato Nollywood. Anan zamu kawo maku wasu daga cikin kyaututtukan da Ali Nuhu ya samu a harkar sa ta shirya fina-finai.[6][7]

ShekaraKyautaRukuniSakamako
2005Arewa Films AwardBest Actor
20073rd Africa Movie Academy AwardsBest Upcoming Actor awardNasara
2008The Future AwardBest ActorNasara
2011Zulu African Film Academy AwardsBest Actor (Indigenous)
20122012 Best of Nollywood AwardsBest Actor (Hausa)Nasara
20139th Africa Movie Academy AwardsBest Supporting ActorNasara
20132013 Nigeria Entertainment AwardsBest ActorNasara
20132013 Best of Nollywood AwardsBest Actor (Hausa)Nasara
2013City People Entertainment AwardsKannywood FaceNasara
2014Kannywood AwardsBest ActorNasara
2014Leadership AwardsBest ArtisteNasara
2014City People Entertainment AwardsBest ActorNasara
2014City People Entertainment AwardsKannywood FaceNasara
2014Arewa Music and Movie AwardsPride of KannywoodNasara
2014Arewa Music and Movie AwardsBest Actor (Popular)Nasara
201519th African Film AwardsMost Outstanding ActorNasara
20152015 Best of Nollywood AwardBest Actor (Hausa)Nasara
20152015 Kannywood AwardsBest Actor (Popular)Nasara
2015City People Entertainment AwardsKannywood PersonalityNasara
20162016 Best of Nollywood AwardsBest Actor (Hausa)Nasara
2016Arewa Music and Movie AwardsBest ActorNasara
2016Kannywood AwardsBest ActorNasara
2016City People Entertainment AwardsKannywood FaceNasara
2016Arewa Creative Industry AwardsEntertainment AwardNasara
2016Wazobia FM’s COWA AwardsExcellent EntertainerNasara
2017Northern Nigeria Peace AwardsBest ActorNasara
2017City People Entertainment AwardsKannywood FaceNasara
2017City People Entertainment AwardsBest ActorNasara
20172017 Best of Nollywood AwardsSpecial Recognition AwardAn dakatar

Hotuna

Ali Nuhu

Manazarta

🔥 Top keywords: