Lawal Kaita

Dan siyasar Najeriya

Lawal Kaita (An haife shi ne a ranar 4 ga Watan Oktoban shekarar 1932) na Miladiyya (A.C) Ya kuma mutu ne a ranar 2 ga watan Janairun shekarar 2018). Ya kasan ce dan siyasan Najeriya ne da aka zaba a jam'iyyar National Party of Nigeria (NPN) a matsayin gwamnan jihar Kaduna, Najeriya, ya rike mukami tsakanin Oktoba zuwa Disamban 1983, lokacin Jamhuriyya ta biyu ta Najeriya wacce ta kare da juyin mulkin da ya kawo Janar Muhammadu Buhari kan mulki.[1][2][3]

Lawal Kaita
gwamnan jihar Kaduna

Oktoba 1983 - Disamba 1983
Abba Musa Rimi - Usman Mu'azu
Rayuwa
HaihuwaKatsina, 4 Oktoba 1932
ƙasaNajeriya
ƘabilaHausawa
Harshen uwaHausa
MutuwaAbuja, 2 ga Janairu, 2018
Yanayin mutuwa (liver failure (en) Fassara)
Karatu
MakarantaKwalejin Barewa
London School of Economics and Political Science (en) Fassara
HarsunaTuranci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'aɗan siyasa

Haihuwa

An haifi Lawal Kaita a ranar 4 ga Oktoban shekarar 1932 a Katsina, Arewacin Najeriya.[4] Shi dan'uwan ​​Shugaba Umaru Musa Yar'Adua ne na jini kuma dan gidan sarautar Nagogo, sarakunan gargajiya na masarautar Katsina. Ya halarci Kwalejin Barewa, Zariya (1946 - 19550) sannan daga baya ya yi karatu a Makarantar Tattalin Arziki ta London (1971–1972).. Bayan dawowarsa Najeriya, Kaita ya zama ma'aikacin gwamnatin jihar Kaduna. Ya yi aiki a matsayin Sakatare a Hukumar Ruwa ta Jiha (1973–1975), Kwamishinan Tsare-Tsaren Tattalin Arziki (1975 - 1977) da Mataimakin Babban Sakatare na Ma’aikatar Ayyuka na Jihar Kaduna (1976–1977).[5][6][7]

Farkon rayuwa

Ilimi

Siyasa

Manazarta

Manazarta


🔥 Top keywords: