So

So tabbas kalmar So nada wata So,nada wata daraja da baiwa wadda ta dade tana bawa malaman soyayya wahala bayyana ta ga dalili kuwa,shine:- Sabanin ra'ayoyin da ake samu daga bangarori dabam dabam na mallaman soyayya ko kuma ince masana soyayya a takaice. Hakan yasa ma'anar So tazo da bayanai dabam dabam, inda wannan dalilin yasa masu karatun littafan soyayya suka kasa gane ainihin ma'anar So. Koda yake So yazo da ma'anoni dabam dabam. Amma zamu iya cewa ma'anar so itace tsananin kauna da bukatar kusantar wani mutum. So", wata iska ce mai yawo wanda babu wani dan adam ko dabba da bai shaketa ba. Kusan ince so hantsi ne leka gidan kowa.Kuma So tsurone, hakana yayi daidai da fadar wani marubuciinda yace"So yakan tsuro har yayi saiwoyinsa a cikin zuciyar masoya, saboda haka idan aka tunbudo shi, shi ma sai ya tunbuko zuciyar. Saboda haka sai in ba'ayi sa'a ba sai a rasa Rai. Sannan Kuma bai kyale kowa ba, ba babba ba, ba yaro ba, ba mutum ba, ba aljani, ba dabba ba kai har tsuntsaye na soyayya!. So yana da hadari idan ba'a yi shi da hankali ba. Ga wasu kirarin So:1. Soyayya ruwan Zuma2. So gubace3. So yayi Kama da Madara4. So mai hana ganin laifi5. So ginshikin rayuwa6. So Hakimin zuciya7. So aljannah duniya da dai sauran su.[1]

simbol ɗin so (love symbol)
hannuwan wasu masoya da suka riƙe juna
Botoramin soyayya na wiki ( cartoon ɗin so na wiki)
Soyayya
advanced emotion (en) Fassara da theme (en) Fassara
Bayanai
Ƙaramin ɓangare naexperience (en) Fassara, affection (en) Fassara da Emotion
Bangare natheory of emotion (en) Fassara da psychology terminology (en) Fassara
Has characteristic (en) Fassaraintimacy (en) Fassara
Hannun riga daKiyayya

Alamomin So kamar haka

  1. Yawan kallo musamman a sace
  2. Yawan Ambato
  3. Faduwar gaba yayi da aka ambata masoyi, kuwa sunan shi.
  4. Yawan tunanin abunda aka kamu da sonshi.
  5. Tausayin: idan kaga mutum Yana yawan tausayin ka to yana sonka
  6. Kunya: idan kaga kunya ta shiga tsakani masoya biyu to akwai soyayya ta gaskiya

Abubuwa dake gyara soyayya

  1. Gaskiya
  2. Amana
  3. Kula
  4. Tsafta
  5. Tsari

Abubuwa dake bata soyayya

1. Karya 2. Yaudara3. Rashin tsafta.4. Rashin yarda da Kuma zargi dadai sauran su.

Manazarta

🔥 Top keywords: