Babban Birnin Tarayya, Najeriya
Babban Birnin Tarayya, anfi saninta da FCT a turance. Ta kasance ita ce babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja. Babban Birnin Najeriyar tana nan ne a tsakiyar ƙasar Najeriya, wanda sanadiyyar ɗauke ta da aka yi daga Legas zuwa inda take a yanzu. An ƙirƙire ta a 1976 daga cikin jihohin tsohuwar ƙasar Kwara, Neja, Kaduna da Plateau tare da mafi yawan ƙasar daga Jihar Neja. Tana nan ne a yankin Middle Belt na ƙasar Najeriya. Ba irin sauran jihohin Najeriya bace, da zaɓaɓɓen Gwamna ke mulka, sai dai ana gudanar da ita ne ta hannun Hukumar Gudanarwar Babban Birnin Tarayya, wanda Minista ke jagoranta ta hanyar naɗa shi daga Shugaban ƙasa.
Babban Birnin Tarayya, Najeriya | |||||
---|---|---|---|---|---|
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | ||||
Babban birni | Abuja | ||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 3,564,126 (2016) | ||||
• Yawan mutane | 487.24 mazaunan/km² | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Yawan fili | 7,315 km² | ||||
Sun raba iyaka da | |||||
Bayanan tarihi | |||||
Mabiyi | Nasarawa, Jihar Neja da Jihar Kogi | ||||
Ƙirƙira | 3 ga Faburairu, 1976 | ||||
Tsarin Siyasa | |||||
Majalisar zartarwa | Hukumar Gudanarwar Babban Birnin Tarayya | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Lamba ta ISO 3166-2 | NG-FC | ||||
Wasu abun | |||||
Yanar gizo | fcta.gov.ng |
buffalo|buffalo]], roan antelope, Western hartebeest, elephant, warthog, grey duiker, dog-faced baboon, patas monkey and green monkey.[1]
Rabe-rabe
Dukda cewa hukumar gudanarwa ta Babban Birnin Tarayya itace keda alhakin gudanar da ayyuka a dukkanin Babban Birnin Tarayya, amma Hukumar Rayawa da Cigaban Birnin Tarayya (FCDA) itace take da ikon akan ayyukan gine-gine da ayyukan cigaba a yankin. Babban Birnin Abuja yana nan ne acikin garin Abuja.[2]
Babban Birnin a yanzu haka yana da ƙananan hukumomi guda shida yankunan hukumomi, namely:[3]
Harsuna
Harsunan dake a Babban Birnin Tarayya, Abuja a kowane ƙaramar hukuma, sune aka jera kamar haka:[4]
Ƙananan hukumomi | Harsuna |
---|---|
Abaji | Dibo; Gupa-Abawa, Egbira, Ganagana |
Abuja Municipal Area Council | Gade; Gbagyi, Nupe, Hausa |
Bwari | Gwandara; Ashe; Gbagyi |
Gwagwalada | Gbari, Egibra, Hausa |
Kuje | Gade; Gbagyi |
Kwali | Gwandara; Gbagyi;Egbira, Kami, Ganagana, Nupe, Hausa |
Manazarta
Haɗin waje
- Babban Birnin Tarayya Archived 2006-05-09 at the Wayback Machine