Dalia Hernández

Dalia Hernández Armenta (an haifeta ranar 14 ga watan Agusta, 1985) ƴar wasan kwaikwayo ce, ta ƙasar Meziko, wadda aka haifa a Veracruz, Mexico.[1] An santa saboda irin rawar ganin da ta taka a cikin fim ɗin Apocalypto (2006),[2] da The Legend of the Maska (2014) da kuma, Miracle Underground (2016).

Dalia Hernández
Rayuwa
HaihuwaVeracruz (en) Fassara, 14 ga Augusta, 1985 (38 shekaru)
ƙasaMexico
Karatu
MakarantaUniversidad Veracruzana (en) Fassara
Sana'a
Sana'aɗan wasan kwaikwayo da dan wasan kwaikwayon talabijin
IMDbnm2199664

A cikin shekarar 2007, ta lashe lambar yabo ta Imagen Award don mafi kyawun goyon bayan ƴar wasan kwaikwayo, duba da rawar da ta taka a fim ɗin Apocalypto.[3] Ya taka rawa a cikin jerin shirin TV masu dogon Zango; "Capadocia del 2008" a cikin kashi na "María Magdalena" inda ya fito a matsayin "Rosa". A cikin 2014 ta taka rawar "Nayeli" a cikin The Legend of the Maska kuma a matsayin "Patricia" a cikin fim ɗin Miracle Underground.

Manazarta