Jerin sunayen Allah a Musulunci

Sunayen Allah ƙyawawa guda casa'in da tara (99)

Jerin sunayen Allah a Musulunci
set of theonyms (en) Fassara
Bayanai
Ƙaramin ɓangare natitle of a particular person or being (en) Fassara

Walilla'hil sama'ul husna, faduhubiha:

LarabciHausa
1Huwallahullaziy la'ilaha illaa huwaShi ne Allah wanda babu wani abin bautawa da gaskiya sai shi
2Arahma'nuMai jin kan muminai da kafirai a duniya
3AlrahimuMai jin kan muminai kadai a lahira
4AlmalikuMamallaki
5AlkuddusuTsarkakken sarki
6AlsalamuMai amintarwa
7AlmuminuAmintaccen sarki
8AlmuhaiminuMai shaida aikin bayi
9Al'AzizuMabuwayi
10AlJabbaruMai gyara bayinsa
11AlmutakabbiruMai girman girma
12AlkhalikuMahaliccin halitta
13AlBari'uMahalicci
14AlMusawiruMai suranta mahaifa
15AlGaffaruMai gafara
16AlKahhaaruMai rinjaye
17AlWahhaabuMai kyauta
18AlRazzaakuMai azurtawa
19AlFattaahuMai budawa bayi
20AlAlimuMasani
21AlKabidhuMai damkewa
22AlBasiduMai shimfida arziki
23AlKhafidhuMai sunkuyarwa
24Al Rafi'uMai daukakawa
25AlMu'izzuMabuwayin sarki
26AlMuzilluMai kaskantarwa
27AlSami'uMai ji
28AlBasiruMai gani
29AlHakmuMai hukunci
30AladaluMai adalci
31AlLadifuMai tausasawa
32AlKhabiruMasanin halittarsa
33AlHalimuMai juriya
34AlAzimuMai girman daraja
35AlGafuruMai gafartawa bayinsa
36AlShakuruSarki abin godewa
37AlAliyuMadaukaki
38AlKabiruMai girman lamari
39AlHafizuMai kiyayewa
40AlMukituMai ciyarwa
41AlHasibuMai iyakancewa
42AlHaliluMai girman girma
43AlKarimuMai madaukakin girma
44AlRakibuMai tsinkayarwa
45AlmujibuMai amsawa
46AlWasiuMai yalwatawa
47AlHakimuMai hikima
48AlWaduduMasoyi
49AlMajiduMai cikakkiyar siffa
50AlBa'isuMai aiko Manzanni
51AlShahiduMai shaida komai
52AlHakkuMatabbacin gaskiya
53AlWakiluMai isarwa
54AlKawiyuMatabbaci
55AlMatinuMai karfi
56AlWaliyuMai jibintarwa
57AlHamiduMacancancin yabo
58AlMuhsiyMai iyakancewa
59AlMubdiyMai bayyanawa
60AlMufiduMai komarwa
61AlMuhyiyMai rayawa
62AlMumituMai kashewa
63AlHayyuRayayyen Sarki
64AlkayyumuMadawwami
65AlWaajiduMai bayarwa
66AlMasjiduMai daukakawa
67AlWahiduMakadaici
68AlSamaduAbin nufi da bukata
69AlKadiruMai iko
70AlMuktadiruMai iko da komai
71AlMukaddimuMai gabatarwa
72AlMuakhkhiruMai jinkirtawa
73AlAuwaluNa farko
74AlAkhiruMarashin karshe
75AlZahiruMabayyani
76AlBadinuBoyayye
77AlWasiyMajibincin lamari
78AlMula'aliyMadaukaki
79AlBarruMai kyautatawa
80AlTauwabuMai karbar tuba
81AlMu'akimuMai ukuba
82Al AfuwuMai rangame
83Al RaufuMai tausasawa
84Malikul MulkiMamallakin mulki
85ZUljalali Wal'IkramiMa'abocin girma da girmame-girmame
86AlMuksiduMai adalci
87AlJaami'uMai tara kowa
88AlganiyuMawadaci
89Al MugniyuMai wadatarwa
90AlMani'uMai hanawa
91Al Dha'ruMai cutar da mai cutarwa
92Al NaafiuMai amfanarwa
93Al NuruMai haskakawa
94Al HadiyMai shiryawa
95Al BadiuMakagi
96Al BakiyWanzajje
97Al WarisuMagaaji
98AlrashiduMai shiryawa
99AlSaburuMai hakuri
🔥 Top keywords: