Kano (jiha)

jiha a Najeriya

Jihar Kano jiha ce da take a Arewa Maso Yammacin ƙasar Najeriya.[1] Tana da yawan faɗin ƙasa kimanin kilomita murabba’i 20,131 da yawan jama’a miliyan sha ɗaya da dubu hamsin da takwas da ɗari uku (a kiyasin shekarar 2011). Babban Birnin jihar shi ne birnin Kano]. Abba Kabir Yusuf ne gwamnan jihar tun daga zaɓen shekarar 2023 har zuwa yau. Ya sami matakin zama gwamna ne a jam'iyyar ''new nigerian people party'' (NNPP). Mataimakin gwamnan shi ne Aminu Abdussalam Gwarzo. Aminu Ado Bayero shi ne Sarkin Kano daga ranar 9 ga watan Maris, 2020 zuwa rana maikamar ta yau. Dattijan jihar sun haɗa da; Aminu Kano, Maitama Sule, Sani Abacha, Murtala Mohammed.

Kano


Wuri
Map
 11°30′N 8°30′E / 11.5°N 8.5°E / 11.5; 8.5
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya

Babban birniKano
Yawan mutane
Faɗi16,076,892 (2016)
• Yawan mutane798.61 mazaunan/km²
Harshen gwamnatiTuranci
Labarin ƙasa
Yawan fili20,131 km²
Sun raba iyaka da
Bayanan tarihi
MabiyiArewacin Najeriya
Ƙirƙira27 Mayu 1967
Tsarin Siyasa
Majalisar zartarwaMajalisar Zartarwa ta Jihar Kano
Gangar majalisaZauren yan majalisar dokokin Jihar Kano
• Gwamnan jihar KanoAbdullahi Umar Ganduje
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
Lamba ta ISO 3166-2NG-KN

Manazarta

🔥 Top keywords: