Bauchi (jiha)

jiha a Najeriya kasar Hausa

Jihar Bauchi jiha ce, da ke Arewa maso gabashin ƙasar Najeriya.Ta hada iyaka daga arewa da Kano da Jigawa, jihar Taraba da Plateau daga kudu, Gombe da Yobe daga Gabas, sai kuma Kaduna daga Yamma. Jihar ta samo asalin sunanta ne daga tarihin masarautar Bauchi, wacce itace babban birnin jihar a yau. An kafa Jihar Bauchi a shekarar alif dari tara da saba'in da shida (1976), a yayin da aka rarraba tsohuwar Jihar Arewa maso Gabacin Najeriya. A baya Jihar Bauchi ta mamaye yankin Jihar Gombe, wacce daga bisani ta zamo jiha mai zaman kanta a shekara ta 1996.[1]

Bauchi


Suna sabodaBauchi
Wuri
Map
 10°30′N 10°00′E / 10.5°N 10°E / 10.5; 10
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya

Babban birniBauchi
Yawan mutane
Faɗi6,834,314 (2016)
• Yawan mutane149.1 mazaunan/km²
Harshen gwamnatiTuranci
Labarin ƙasa
Yawan fili45,837 km²
Sun raba iyaka da
Bayanan tarihi
MabiyiJihar Arewa maso Gabas
Ƙirƙira3 ga Faburairu, 1976
Tsarin Siyasa
Majalisar zartarwaexecutive council of Bauchi State (en) Fassara
Gangar majalisaMajalisar Dokokin Jihar Bauchi
Bayanan Tuntuɓa
Lambar aika saƙo740001
Kasancewa a yanki na lokaci
Tsarin lamba ta kiran tarho+234
Lamba ta ISO 3166-2NG-BA
Wasu abun

Yanar gizobauchistate.gov.ng
Twitter: BauchiState Edit the value on Wikidata
masarautar Bauchi
bauchi
Al'ummar bauchi a wajen bukukuwan al'ada
Federal government of Bauchi

Bauchi itace jiha ta biyar a fadin kasar, kuma ta bakwai a yawan jama'a. Ta na da yawan fili kimanin kilomita dubu ar,ba’in da tara da dari dagoma shatara (49,119) da yawan Jama’a miliyan shida da dubu dari biyar da dubu talatin (6,530,000) a bisa kidayar shekara ta dubu biyu da sha shida 2016. Jihar ta rabu dangane da yanayin kasa zuwa kashi biyu (2), West Sudanian savanna daga kudu da kuma semi-desert sahel Savanna daga arewa, da kuma montane Jos Plateau daga kudu maso yammacin Jihar.[2] Daga cikin kayatattun wurare a garin sun hada da, Yankari National Park, wani katafaren wajen ajiye dabbobi ne dake kudancin jihar Bauchi inda akwai dabbobi kaman bijimai, birrai, barewa, zakuna, giwaye da dai sauransu.[3]

Bauchi ne babban birnin jihar Bauchi. Bala Abdulkadir Mohammed shi ne Gwamnan jihar tun zaben shekara ta 2019 har zuwa yau. Wasu daga cikin dattijan Jihar sun hada da: Abubakar Tafawa Balewa, Isa Yuguda, Isah Hamma Misau, Nazif Gamawa, Haruna Ningi da Ali Wakili.

Akwai yaruka da dama a yankuna daban daban na Jihar wadanda suka hada da: Yaren Bolewa, Butawa, da Yaren Warji daga yankunan tsakiyar jihar; Yaren Fulfulde, Yaren Kanuri, da Yaren Karai-Karai daga arewacin garin; Fulani da Yaren Gerawa acikin birnin Bauchi da kewayen ta; Yaren Zaar (Sayawa) daga kudu; Yaren Tangale daga kudu maso gabas; da kuma Jarawa daga kudu maso yamma. Mafi akasarin mutanen gari (kaso tamanin da biyar 85%) musulmai ne, da karamin kaso kiristoci da kaso shida 6% da maguzawa da kaso tara 9%.[4]

A farkon shekarun alif dubu da dari takwas 1800s, Fulani Jihadi sun kwace mafi akasarin garin birnin Bauchi na yau, sannan suka kafa Masarautar Bauchi a karkashin Daular Masarautar Musulunci na Sokoto. A karni na dubu daya da shatara 1900 ne Turawan mulkin mallaka suka mamaye Masarautar kuma suka hade ta a cikin Yankin Mulkin Mallaka na Arewacin Najeriya wacce daga bisani ta zamo Najeriya karkashin mulkin Turawa, kafin samun 'yanci a shekarar alif dari Tara da sittin 1960. Tun asali, yankin Jihar Bauchi a yau tana cikin Yankin Arewa bayan samun 'yanci har zuwa shekarar alif ta 1967 lokacin da aka raba yankin kuma jihar ta fada karkashin Jihar Arewa ta Gabas.[5] Bayan rarraba Jihar Arewa ta Gabas, an kafa Jihar Bauchi a ranar uku 3 ga watan Februrun shekara ta dubu daya da dari tara da saba'in da shida 1976 tare da sauran jihohi goma. Shekaru ashirin (20) kuma bayan kafata, an hade wasu kananan hukumomi daga yammacin Jihar inda suka samar da Jihar Gombe.

A matsayinta na jihar da ta dogara da noma, tattalin arzkin Jihar sun ta'allaka ne akan dabbobi da hatsi, kamansu auduga, gyaɗa, dawa, tumatiri da kuma doya tare da cigaba a fannin noman rani na kara habaka samar da abinci tun zamanta jiha. Sannan akwai masana'antu na sarrafa abinci da masana'antun sarrafa kayan abinci na gwan-gwani, da kuma hako ma'adanai kamar tin da columbite, da kuma wuraren bude idanu kamar Dajin shakatawa na Yankari da koramunta na Wikki Springs.[6]

Asalin Suna

Dangane da tarihi na gargajiya, garin ya samo asali ne daga wani mafarauci mai suna Baushe, wanda ya zauna a yankin kafin zuwan jagoran masarutar na farko wato Yakubu (wacce aka samar a tsakanin alif ta 1800–10).[7] Jihohin Bauchi da Adamawa sun kasance kasashen 'yanci da kasuwanci ga mutanen Daular Fulani na Sokoto.[8]

Tarihi

Bauchi a Shekarar 1970

Wurin da ake kira Bauchi ta kasance kafin shakarar alif ta 1976 gunduma a yankin Jihar Arewa ta Gabas. Danagne da kidayar shekara ta 2006, Jihar tana da mutane kimanin 4,653,066.

Jihar Bauchi ta sama cigaba iri-iri a cikin 'yan shekarun nan. Akwai harshen Ajawa da akayi amfani dashi a jihar Bauchi, amma daga bisani ya bace a tsakanin shekarun 1920 da shekara ta 1940 inda asalin masu amfani da harshe suka sauya zuwa Hausa.[9]

A lokacin mulkin Turawa har zuwa samun 'yanci, tana cikin yankin Plateau da Yankin Arewacin Najeriya, har zuwa 1967 lokacin da aka samar da jihohi, yayin da yankunan Bauchi, Borno, da Adamawa suka hade wajen samar da Jihar Arewa ta Gabas.

Bayan samar da Jihar Bauchi a shekara ta 1976, a lokacin Jihohi biyu Bauchi da Gombe na hade, jihar nada kananan hukumomi 16. Daga bisani an kara yawan kananan hukumomin zuwa 20 sannan daga bisani 23. Haka zalika, a shekara ta 1997, an samar da Jihar Gombe, daga Jihar Bauchi inda aka samu karin kananan hukumomi a kasar, inda aka bar Jihar Bauchi da kananan hukumomi 20 kamar yadda aka zayyano a kasa:

Kananan Hukumomi

Jihar Bauchi nada adadin Kananan hukumomi ashirin (20). Sune:

Karamar HukumaFadin kasa (km2)Adadin 2006
Mutane
Cibiyar Karamar HukumaLambar aika
sako
Bauchi3,687493,810Bauchi740
Tafawa Balewa2,515219,988Bununu740
Dass53589,943Dass740
Toro6,932350,404Toro740
Bogoro89484,215Bogoro741
Ningi4,625387,192Ningi742
Warji625114,720Warji742
Ganjuwa5,059280,468Kafin Madaki742
Kirfi2,371147,618Kirfi743
Alkaleri5,918329,424Alkaleri743
Southern region totals33,1612,497,782
Darazo3,015251,597Darazo750
Misau1,226263,487Misau750
Giade668156,969Giade750
Shira1,321234,014Yana750
Jama'are493117,883Jama'are751
Katagum1,436295,970Azare751
Itas/Gadau1,398229,996Itas751
Zaki1,476191,457Katagum752
Gamawa2,925286,388Gamawa752
Damban1,077150,922Damban752
Northern region totals15,0352,178,683

Garuruwa

Bauchi Emirate Council

Kirfi Ta kasance Garine cikin Birnin Bauchi wanda keda aƙalla faɗin aƙalla 700 meters kewaye da gefenta ne rafin Gongola wanda ke isar da ruwa zuwa cikin garin. Wanda ya haɗe da babban kogin Benue. Gari ne mai tarin albarkoki, a ɓangaren Noma da Kiwo.[10] A al’adance ta kasance tana maraba ne kaɗai da mutanen da ake kira Kirfawa kuma ta faɗa ƙarƙashin gundumar Hausawa. Bincike akan garin Kirfi ya nuna cewa amsoshin da suka ƙunshi al’ada, da Addini da harkan Siyasa a ƙasar Hausa ana iya samun sa a garin Kirfi ta garin Bauchi.[10]

Labarin kasa

Jihar Bauchi ta mamaye fadin kasa kimanin 49,119 km2 (18,965 sq mi) inda ta mamaye kaso 5.3% na daukakin fadin Najeriya kuma tana zaune akan lambobin wuri na latitudes 9° 3' da 12° 3' arewa da kuma longitudes 8° 50' da 11° gabas.

Jihar tana da iyaka da jihohi bakwai, Kano da Jigawa daga arewa, Taraba da Plateau daga Kudu, Gombe da Yobe daga Gabas sai kuma Kaduna daga Yamma.

Jihar Bauchi na daga cikin jihohin arewan Najeriya dake da yanayin tsirrai iri biyu, Sudan savannah da kuma Sahel savannah. Haka zalika akwai tsaunuka a kudancin yankin garin, dangane da alakarta da tsaunukan Jos Plateau.

Adadin jama'a

Akwai Kabilu daban daban har guda 55 a garin wanda suka hada da: Gerawa, Sayawa, Jarawa, Kirfawa, Hausawa Bolewa, Karekare, Kanuri, Fa'awa, Butawa, Warjawa, Zulawa, Boyawa, Badawa. Amma Fulani ne asalin kabilar garin. Hakan na nufin cewa suna da nasu asalin, al'adu, addinai da makamantansu.

Akwai kamaiceceniya tsakanin harsunan garin, dangane da ayyuka, al'adu, sutura, da kuma cudanya a tsakaninsu musamman ta hanyar auratanya da kasuwanci. Wasu daga cikin harsunan na da ba'a a tsakaninsu. da Sayawa da dai sauransu.

Bikin hawan sallah na daya daga cikin muhimman bukukuwa da ke jawo 'yan kallo a duk shekara.[11]

Ilimi

Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa[12] na nan acikin babban birnin Bauchi.[13] Wasu daga cikin wuraren koyarwa sun hada da; Jami'ar Jihar Bauchi,[14] Abubakar Tatari Ali Polytechnic[15] , Federal Polytechnic, Bauchi.[16], Aminu saleh college of Education Azare[17]Federal university of health science Azare[18]

Yaruka

Ire-iren harsunan West Chadic language da ake amfani dasu a Bauchi sun hada da:[19]

Yarukan Bauchi a jere da kananan hukumominsu.[20]

LGALanguages
AlkaleriDass; Bole; Duguri; Giiwo; Guruntum-Mbaaru; Labir; Tangale
BauchiBankal; Duguri; Dulbu; Galambu; Gera; Geruma; Giiwo; Guruntum-Mbaaru; Ju; Kir-Balar; Labir; Luri; Mangas; Mbat; Pa'a; Polci; Shiki; Tala; Zangwal
BogoroSaya
DarazoBole; Deno; Diri; Giiwo; Mburku; Ngamo; Zumbun
DassBankal; Dass; Gwak; Polci; Saya; Shall-Zwall; Zari
DukkuBole
GamawaKarekare
GanjuwaCiwogai; Gera; Geruma; Jimi; Kariya; Kubi; Miya
KirfiBure
MisauFulato/Borno; Shuwa; Kanuri; Hausa; Fulani
NingiDiri; Gamo-Ningi; Kudu-Camo; Pa'a; Siri; Warji; Geruma
Tafawa BalewaSur; Vaghat-Ya-Bijim-Legeri; Zari; Bankal; Gwak; Izere; Saya
ToroBankal; Dass; Geji; Geruma; Gwa; Gyem; Iguta; Izere; Jere; Lame; Lemoro; Mawa; Panawa; Polci; Sanga; Saya; Shau; Tunzuii; Zari; Zeem; Ziriya
ZakiBade

Sauran harsunan Bauchi sun hada da: Ajawa, Beele, Berom, Kanuri, Kwaami, Manga, Pero, da kuma Piya-Kwonci.

Gwamnati

Gwamnan garin shine babban mai zartarwa, tare da fannin shari'a na garin na nan a birnin Bauchi.[21]

Gwamna

Gwamna Bauchi shine Mr. Bala AbdulKadir Mohammed, wanda ya lashe zabe a ranar 9 ga watan March,shekara ta 2019 a karkashin jam'iyyar PDP. An rantsar dashi a ranar May 29, ga watan shekara ta 2019, wanda hakan tasa ya zamo gwamna na shida a Bauchi a karkashin mulkin dimukradiyya sannan kuma gwamna na 16 gaba daya. Baba Tela ne mataimakin gwamnan Bauchi.[22][23]

Kiwon Lafiya

Jihar Bauchi na da tarin asibitoci daman hukumomin kiwon lafiya, wannnan sun hada da:

  • Abubakar Tafawa Balewa Teaching Hospital[24][25]
  • Bauchi State Hospital
  • Al-amin Hospital
  • Niima Consultants Hospital
  • Albishir Clinic and Maternity
  • Proactive Clinic and Hospital Ltd.

Sanannun Mutane

Bibiliyo

  • Haour, Anne., Rossi, Benedetta (2010) Being and becoming Hausa : interdisciplinary perspectives.Leiden: Brill. ISBN 978-90-04-1854-25
Gidan namun daji na bauchi
manyan mutane a bauchi, Tsohon gwamnan jihar Barr Muhammad Abubakar

Manazarta


Jihohin Najeriya
Babban birnin tarayyar (Abuja) | Abiya | Adamawa | Akwa Ibom | Anambra | Bauchi | Bayelsa | Benue | Borno | Cross River | Delta | Ebonyi | Edo | Ekiti | Enugu | Gombe | Imo | Jigawa

Kaduna | Kano | Katsina | Kebbi | Kogi | Kwara | Lagos | Nasarawa | Neja | Ogun | Ondo | Osun | Oyo | Plateau | Rivers | Sokoto | Taraba | Yobe | Zamfara

🔥 Top keywords: