Masjid al-Haram

Babban Masallacin Makkah (da larabci; ٱلْـمَـسْـجِـد ٱلْـحَـرَام a furucci; al-Masjid al-Ḥarām a ilimance; Masallaci mai Tsarki, da turanci; The Sacred Mosque)[1]) shine masallacin daya zagaye Kaaba dake birnin Mecca, Saudiya. Wuri ne na ziyara domin aikin hajji, wanda kowane Musulmi dole ya aikata shi, karanci sau daya a rayuwarsa idan yana da ikon zuwa, wanda aikin yahada da kewaye dakin Kaaba dake a cikin masallacin. Kuma nan muhimmin wurin yin ‘Umrah, karamin aikin hajji da akeyi a kowane lokaci a cikin shekara. Babban masallacin yahada da wasu mahimman wurare, wadanda suka hada da, Baƙin Dutse, Rijiyar ZamZam, wurin tsayuwar annabi Ibrahim, da duwatsun Safa da Marwa.[2] A bude Masallacin yake, akowane lokaci da yanayi.

Masjid al-Haram
المسجد الحرام
Wuri
Ƴantacciyar ƙasaSaudi Arebiya
Province of Saudi Arabia (en) Fassarayankin Makka
Tourist attraction (en) FassaraMakkah
Coordinates21°25′21″N 39°49′34″E / 21.4225°N 39.8261°E / 21.4225; 39.8261
Map
History and use
Grand Mosque Seizure

Aikin Hajji

Umrah

Start of manufacturing 630
AddiniMusulunci
Maximum capacity (en) Fassara820,000
Karatun Gine-gine
Style (en) FassaraIslamic architecture (en) Fassara
Tsawo137.5 m
PartsHasumiya: 9
Offical website
Masallacin Harami lokacin aikin Hajji na shekarar 2009
Alhazai suna addu'a a masallaci mai alfarma
hoton masallacin Madinah
masulmai a cikin masallaci mai alfarma
Sheikh Sudais limamin masallaci mai alfarma
masallaci Mai tsarki Makkah
Ruwwaqul Usmani a cikin masallaci mai tsarki
masallaci mai tsarki a shekarar 1969
cikin Masallaci mai tsarki
Alhazai na ɗawafi a Ka'aba masallaci mai tsarki
Babban masalacin makka
masallacin Madinah a shekarar 1908

Babban Masallacin harami shine masallaci mafi girma a duniya, kuma anmasa gyararraki da faɗaɗa shi a lokuta daban-daban a shekaru.[3] Ta wuce lokuta da dama ƙarƙashin kulawar Halifofi daban-daban, sultans da sarakuna, kuma ayanzu babban masallacin na ƙarƙashin kulawar Sarkin Saudi Arabia wanda shine Custodian of the Two Holy Mosques.[4] Tana nan ne a gaban Abraj Al Bait, mafi tsayin ginin agogo a duniya,[5] aikin gininsa dake cike da cece-kuce akan rushe wuraren tarihi na farkon musulunci da gwamnatin Saudiya tayi.[6]

masallacin Makkah mai tsarki a shekarar 1889

Manazarta

🔥 Top keywords: