Nicola Lechner

Nicola Lechner 'yar Austriya ce ta 'yar wasan zamiya na ƙanƙara wato Paralympic alpine skier. Ta wakilci ƙasar Austriya a gasar tseren zamiya na Alpine a wasannin Paralympic Winter Games na 1998 a Nagano, da wasannin zamiya na 2002 a Salt Lake City. Ta lashe lambobin yabo guda biyar: lambobin azurfa uku da tagulla biyu.[1]

Nicola Lechner
Rayuwa
ƙasaAustriya
Sana'a
Sana'aalpine skier (en) Fassara
Hoton zamiya na nakasassu

Aiki

A gasar wasannin motsa jiki nazamiyar na 1998, a Nagano, Japan, Lechner tayi nasara a wasanni hudu. Ta ci azurfa a cikin slalom (a cikin lokacin 2:06.22, zinariya ga Sarah Billmeier a 2:04.99 da tagulla ga Maggie Behle a 2: 08.14),[2] giant slalom (tare da 2:49.10 Lechner ta ci Sarah Billmeier a 2:49.44, amma ta kare a bayan dan uwanta Danja Haslacher a 2:47.70),[3] da kasa (a 1:14.95, ta kare a bayan Sarah Billmeier, ta 1st a 1:14.79, amma gaba da Maggie Behle, a matsayi na 3 a 1:18.04).[4] Ta ci lambar tagulla a tseren super-G LW2, a cikin 1:09.06 (zinariya ga Danja Haslacher da lokacin 1:08.80, da azurfa ga Sarah Billmeier a 1: 09.04).[5]

A wasannin zamiya na 2002 da aka gudanar a Salt Lake City kuwa, a cikin 2:32.95, Lechner ta gama matsayi na 3 a cikin giant slalom na LW2, a bayan 'yar ƙasar Danja Haslacher a 2:24.85 da Ba’amurke Allison Jones a 2:32.55.[6] Ta kare na hudu a gasar mata ta kasa LW2,[7] da mata super-G LW2.[8] Ba ta samu kammala tseren ba a gasar slalom ta mata LW2.[9]

Manazarta

🔥 Top keywords: