Apapa

Apapa Karamar hukuma ce dake a wacce ke yammacin tsibirin Lagos a Jihar Lagos, Nijeriya. A cikin Apapa akwai tashoshin jiragen ruwa da dama kuma suna gudanar da ayyukansu a karkashin Nigerian Port Authority (NPA) wanda suka hada da aininhin tashar jiragen ruwa na Lagos da kuma tashar Lagos Port Complex (LPC).[1]

Apapa


Wuri
Map
 6°26′56″N 3°21′32″E / 6.4489°N 3.3589°E / 6.4489; 3.3589
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
JihaLagos
Ƙaramar hukuma a NijeriyaApapa (en) Fassara
Yawan mutane
Faɗi217,362
Labarin ƙasa
Bangare naSouthwest Nigeria (en) Fassara
Bayanan Tuntuɓa
Lambar aika saƙo101252
Kasancewa a yanki na lokaci

Bayani

Karamar hukumar Apapa tana nan kusa da tafkin Lagos (watau Lagos Lagoon), sannan kuma akwai nau'ikan kaya kala kala kaman kwantenoni da cargo-cargo, gidaje, ofisoshi da wata tsohuwar titin jirgin kasa wacce bata aiki a yanzu a arewacin Apapa. Itace kuma ainihin kafar shigo da kayayyaki na Najeriya har zuwa 5 ga watan Mayun shekara ta 2005 lokacin da ta koma karkashin kungiyar sufuri ta ruwa watau Danish firm A. P. Moller-Maersk Group. [2]Sannan daura da wannan tashar akwai tashar jiragen ruwa na Tin Can Island Port (TCIP).[3]

Har wayau akwai matatan man-fetur a cikin Apapa kamar Bua Group. Sannan akwai ofisoshi manymanya na kasuwanci sufurin kaya zuwa wurare daban daban a duniya. Daga cikin sanannun gine-gine akwai Folawiyo Towers. Acikin Apapa akwai hedikwatoci da dama kamar hedikwatan gidan jarida na Najeriya watau Thisday.[4]

Tarihi

An tsinci wani sarakar tagulla a karni na 16 wanda a yanzu haka yana nan a jiye a gidan tarihi na British Museum.Acikin shekara ta 2015 aka kaddamar da aikin ginin gidajen zamani a fili me fadin eka 1000. An kammala aikin ginin a tsakanin shekarun 1957/1958 kuma ta wanzu tare da fadada Apapa Wharf. Gidajen sun kunshi tarin ma'aikatan kamfanoni musamman na gine-gine da sauransu. Makarantar German School Lagos tana Apapa a da.[5]

Gidajen da kayan Gwamnati

Gidaje da wuraren karatu

A cikin Apapa akwai gidaje iri-iri kama daga na alfarma masu tsada har da matsakaita tsada da saukin kudi.[6]

Akwai wuraren shakatawa iri-iri kamar wurin hawa jirgin ruwa na zama a Apapa Creek.

Manazarta