Bayt Al-Suhaymi

Bayt Al-Suhaymi ("Gidan Suhaymi") gida ne na Islama na Masarawa na Gargajiya da kuma gidan kayan gargajiya a Alkahira, Masar. Abdel Wahab el Talawy ne ya gina shi a shekara ta dubu ɗaya da ɗari shida da arba'in da takwas 1648 [1] tare da Darb al-Asfar, wani yanki mai daraja da tsada a Alkahira. A cikin shekarar 1796 Sheikh Ahmed as-Suhaymi ne ya siya shi wanda danginsa suka rike ta na wasu tsararraki masu zuwa. Shehin Malamin ya fadada gidan sosai tun daga asali ta hanyar shigar da gidaje makwabta cikin tsarinsa.[2]

Bayt Al-Suhaymi
Wuri
Ƴantacciyar ƙasaMisra
Governorate of Egypt (en) FassaraCairo Governorate (en) Fassara
Coordinates30°03′08″N 31°15′45″E / 30.0522°N 31.2625°E / 30.0522; 31.2625
Map
Karatun Gine-gine
Style (en) FassaraIslamic architecture (en) Fassara

An gina gidan a kusa da wani sahn da ke tsakiyarsa akwai wani dan karamin lambu mai tsiro da dabino. Daga nan ana iya ganin tagogi masu kyau na masharabiya a gidan. A yau gidan kayan gargajiya ne wanda baƙi na ƙasashen waje za su iya zagayawa akan fam 35 na Masar (15 ga ɗalibai). Yawancin aikin bene na marmara, kayan katako, da kayan adon rufi har yanzu suna nan. Maidowa ya faru bayan girgizar kasa na shekarar 1992.[3]

Manazarta

Hanyoyin haɗi na waje