Camille Koenig

Camille Koenig (an haife ta ranar 23 ga watan Yuni 2001)[1] 'yar wasan ninkaya ce ta Mauritius.

Camille Koenig
Rayuwa
Haihuwa23 ga Yuni, 2001 (22 shekaru)
ƙasaMoris
Sana'a
Sana'aswimmer (en) Fassara

A cikin shekarar 2019, ta wakilci Mauritius a gasar cin kofin ruwa ta duniya na shekarar 2019 da aka gudanar a Gwangju, Koriya ta Kudu. Ta fafata ne a gasar tseren salo na mita 50 na mata. [2] Ba ta samu damar shiga wasan kusa da na karshe ba. [2] Ta kuma fafata a gasar tseren baya ta mata na mita 200 kuma a wannan karon ma ba ta tsallake zuwa matakin kusa da na karshe ba.[3] A shekarar 2019, ta kuma wakilci kasar Mauritius a gasar wasannin Afrika na shekarar 2019 da aka gudanar a birnin Rabat na kasar Morocco ba tare da samun lambar yabo ba.[4]

Manazarta