Cheick Fantamady Camara

Cheick Fantamady Camara (1960 - Janairu 7, 2017) darektan fina-finan Guinea ne wanda ya lashe lambar yabo. Ya kasance darakta na gajerun fina-finai guda biyu da kuma fina-finai guda biyu. Fim ɗin sa na shekarar 2006 Il va pleuvoir sur Conakry ya lashe gasar Fim da Talabijin na Panafrica na 2007 na Ouagadougou a Burkina Faso da Prix Ousmane Sembène na 2008 a bikin Khoribga African Cinema Festival a Morocco.

Cheick Fantamady Camara
Rayuwa
HaihuwaConakry, 12 ga Maris, 1960
ƙasaGine
Mutuwa10th arrondissement of Paris (en) Fassara, 6 ga Janairu, 2017
Karatu
MakarantaÉcole nationale supérieure Louis-Lumière (en) Fassara
HarsunaFaransanci
Sana'a
Sana'adarakta da marubin wasannin kwaykwayo
Imani
Addinianimism (en) Fassara
IMDbnm0131162

Rayuwar farko

An haifi Cheick Fantamady Camara a cikin 1960 a Conakry, Guinea.[1][2] Yayin da yake zaune a Faransa yana da shekaru 40, ya ɗauki kwas a rubuce-rubucen fim a Institut national de l'audiovisuel, ya kammala karatunsa a shekarar 1997. [1] [2] Bayan shekara guda, a cikin 1998, ya yi karanci ba da umarni na fim a Kwalejin Louis Lumière. [1] [2]

Mutuwa

Camara ya mutu ranar 7 ga watan Janairu, 2017, yana da shekaru 57 a duniya.

Nassoshi

Hanyoyin Hadi na waje