Jinin Haida

Jinin Haida((حيض)) to muna farawa da sunan Allah maiRahma mai Jinkai, tsira da amincinAllah su kara tabbata ga fiyayyan halittar AllahAnnabin tsira Annabi Muhammad, da Iyalanshi da Sahabban shi baki daya.[1][2] Bayanhaka ga wasu dagaabinda ya shafi hukunce-hukuncenjinin al'ada wanda ake kira Jinin haida, yana da matukar muhimmancisanin hukunce-hukuncen jinin al'ada,muhimmancin ba wai ya tsaya ga mata banekadai a'a har da maza, domin abubuwa dayawa na ibada da na zamantakewa sunada alaka da jinin al'ada, misali mai jininal'ada bata sallah ko azumi ko dawafi,wannan bangaran ibada kenan amma tabangaren zamantakewa mai jinin al'ada ba'asakinta idan Kuma aka yi sakin to ya tabbatar, ba kuma a saduwa da ita, sannanga yadda Allah ya sanya idda da jininal'ada, ta yadda idan aka saki mace sai taga tsarki uku (al'ada uku) kafin aka ce takammala iddah sannan ai maganar sabonaure, to idan tana al'ada bayan kowadannewatanni shida kenan sai bayan shekaradaya da rabi za'a fara maganar aure, shiya sa muka ce sanin hukunce-hukuncenwannan jinin ba wai ya rataya ga matabane kadai har da maza.[3][4].

Jinin Haida
biological process (en) Fassara
Bayanai
Ƙaramin ɓangare namenstruation (en) Fassara
Facet of (en) Fassarahuman reproduction (en) Fassara da women's health (en) Fassara
Found in taxon (en) FassaraHomo sapiens (en) Fassara
Shafin yanar gizobacsisaigon.net… da bacsisaigon.net…
WordLift URL (en) Fassarahttp://data.thenextweb.com/tnw/entity/menstruation

Masana sun kayyade cewa lafiyayyen jinin al'ada yakan shafe kwanaki huɗu (4) zuwa kwanaki bakwai (7) yana zuba sannan ya dauke, idan ya dauke yakan shafe kwanaki ashirin da daya (21) zuwa kwanaki talatin da biyar (35) kamin kuma ya sake [1].[5]

Menene Jinin Al'ada

Jinin al'ada jini ne dayake fita da karan kansa daga gabanmacan da a al'adance zata iya daukar cikiba tare da ya wuce kwanaki goma sha-biyarba.Wannan shi ake nufi da jinin al'ada, daaka ce 'jinine da yake fita da kansa' kenanidan ya zamana ba da kansa ya fita bakamar ace cinnaka ya cije ta a gaba kokunama sai jinin ya balle mata to wannanbai zama jinin al'adaba.Da aka ce 'Ta gaba' kenan idan ya fitata dubura ko ta hanci wannan bai zamajinin al'adaba. Da aka ce wacce aal'adance zata iya daukar ciki kenan idanya fita daga wacce a al'adance ba zata iyadaukar ciki ba sabo da yarinta ko girma towannan shi ma bai zama jinin al'ada ba.Amma da aka ce 'Ba tare da ya wucekwanaki goma sha biyar ba, kenan idan yawuce kwanaki sha biyar (15) to bai zamo kumajinin al'adaba.Wadannan nau'uka da akace basu zamajinin al'ada ba kenan hukuncin jinin al'ada baihau kansu ba za su yi sallah domin jininciwo ne sai a nemi magani, Allah yasawwake.

Mafi Karancin sa

Malamai sun karawa junasani kan mafi karancin jinin al'ada, mafikarancinsa shi ne dugo guda ɗaya kenan idanya ɗiga sannan ya ɗauke, shi kenan ta yial'ada kuma ta dauke.

Mafi Yawansa

Mafi yawan kwanakin jininal'ada shi ne kwanaki goma sha-biyar kenanidan ya wuce haka to bai zama jininal'ada ba muddin ba ciki take da shiba. Mata Dangane da Al'ada: anan mun sanimata suna da halaye biyar musamman idanmuka yi la'akari da shekarunsu domin aunajinin da ya zo na al'adane ko bana al'adaba ne, kamar haka:

  1. Kasa da shekara tara Idan jinin ya

zo wa yarinyar da take kasa da shekaratara to malamai sun tabbatar da wannanba jinin al'ada ba ne, jinin ciwo ne sai a nemimagani.

  1. Tara Zuwa Sama Idan ya zamana jinin ya

zo ne ga wacce ta cika shekara tarazuwa zamanta budurwa, to a irin wannanlokaci sai a tambayi kwararrun mata dalikita domin a fayyace jinin na al'adane kona ciwo. Kada mu sha'afa yanayin abinci dakuma yanayin zafi da sanyi da hutu dawahala suna tasiri.

  1. Budurci Zuwa Sheka 50 Idan jinin ya

zo daga lokacin da ta zama budurwa zuwashekaru hamsin (50) kai tsaye malamai suntabbatar da cewa wannan jinin na al'adane.

  1. Daga 50 - 69 Idan jini ya zo wa mace

a tsakanin wadannan shekaru wato dagashekara hamsin zuwa sittin da tara(50-69) to malamai suka ce za'a tambayikwararrun mata da likitoci domin saninwannan jinin na ciwone ko na al'ada.

  1. Daga 70 Idan jini ya zo bayan mace ta

cika shekara saba'in (70) zuwa sama tomalamai suka ce wannan kai tsaye ba jininal'ada bane.Ashe tantance shekarun haihuwa bakaramin abu bane domin tuni musulunci yagina hukunce-hukunce a kansu, kuma anagini ne a kan tsarin kalandar musulunci,wadannan bayanai na karkasuwar mata harzuwa gida biyar kamar yadda ya gabatahaka malam Adawi ya kawo a cikinlittafinsa 'Hashiyatul Adawi', Allah ya jikansa da gafara.Ina daɗa jaddada cewa yanayin abinci dada abin sha da sanyi ko yanayin zafi sunatasiri matuka, dukkan abinda ba'a fahimta ba dangane da yana yin zuwanjinin ko daukewarsa yarinyace ko babba tokamata ya yi ayi tambaya cikin gaggawalura da yadda muka yi bayai da cewayana da alaka da hukunce-hukunce, kina yinjinkiri sai salloli su kubuce miki, kumawannan yana nuna cewa mace da aka sakazata iya kammala idda akasa da watanniuku.Idan yarinya ta ga jinin kuma jinin yazama shi ne zuwansa na farko sannan yatabbata cewa jinin al'adane to ta sani tabalaga, dukkanin hukunce-hukuncenmusulunci sun hau kanta, idan ta yi salatinAnnabi za'a rubuta mata lada idan kuma tabari samari suna jagwalgwalata ita za'arubutawa zunubi, ba wanda yace wai sai tayi aure sannan za'a fara yi mata rubutu,kenan har azumi sai ta ranka wanda tasha.

Tabbatuwar Jinin Al'ada

Shifa abin da yashafi jinin al'ada al'amari ne da Allahmaɗaukakin sarki ya yi bayaninsa a cikinAlkur'ani mai girma, Allah yana cewa:Kuma suna tambayarka dangane daal'ada, Kace: Shidinnan cutane, ku nisanci(saduwa da) mata a lokacin al'ada, kadaku kusance su har sai sun yi tsarki (Jininya dauke) idan suka tsarkaka (suka yiwanka) to ku je musu ta inda Allah yaumarceku, Lalle Allah yana son masuyawan tuba kuma yana son masutsarkaka. Bakara, ayata: 222.Haka kuma ma'aikin Allah –Tsira daamincin Allah su kara tabbata a gareshi- yace;(Wannan) Wani abu ne da Allah ya dorawamata 'ya'yan Adam. Ashe ba shaci-fadinda ake cewa ba ne ai sanadiyyar da yasamata suke al'ada shi ne wannan ganyanbishiyar da Nana Hawwa'u ta ci a gidanaljanna, amma Annabi Adam mala'ikane yarike masa makoshi (makogaro) sai yaamayar da abin shi ya sa maza basa yi.Wannan labarin bashi da kanshin gaskiyadomin ayoyin Alkur'ani sun tabbatar daAnnabi Adam ya ci itaciyar.Shi fa jinin al'ada kada amanta jini ne dayake fitowa daga can cikin mahaifa alokuta sanannu, Allah madaukakin Sarki yahaliccishi domin ya zama abinci ga yaro alokacin da yake cikin mahaifiyarsa domininda zai yi tarayya da mahaifiiyar ta shi aabincin da take ci to da karfinta ya ragusosai,sa Allah ya sanya shi ya zama abincigareshi,shi ya sa da kyar ka ga macetana da juna biyu (ciki) kuma tana al'ada.Idan kuma ta haihu sai Allah ya zamar dashi nono jaririn yana sha amatsayin abinci,shi yasa kadan ake samun matan dasuke shayarwa kuma suna al'ada. Idan yazamana mace bata da juna biyu (ciki) kumabata shayarwa sai ya kasance ba inda zaije to shi ne sai ya taru a mahaifarta,shi nemafi yawancin lokuta yake fita a kowannewata cikin kwanuka shida ko bakwai, ya kankaru ko ya ragu akan hakan kamar yaddabayanai za su zo da izinin Allah-gwargadon yadda Allah ya tsara halittarsa.

wannan yadda jinin al'ada yake kwarara kenan daga jikin wata baturiya

.

Karkasuwar Mata

Mawallafin littafinAkhadari ya kasa mata zuwa kashi ukudangane da jinin al'ada, kashi na farko;ita ce wacce ta fara, kashi na biyu kuma;wacce ta saba, sannan sai kashi na uku;mai juna-biyu (wato mai ciki), ga bayanansukamar haka:

digon Jinin al'ada
  1. Wacce Ta Fara Ita wacce ta fara

al'ada ya zama yinta na yanzu shi ne ganinal'adarta na farko a rayuwarta, to abin da yake kanta zata zuba ido ne ta ga kwanakinawa zai dauka kafin ya yanke, ta yadda bazai wuce kwanaki sha-biyar ba, idan ko yawuce sha-biyar to abinda ya doru akankwanaki sha-biyar bai zama al'ada ba, kenanmafi yawan kwanakin da zata saurara sunekwanaki sha-biyar, amma zai iya daukewakafin hakan, abin nufi in ya wuce to yazama (Istihadha) cuta sai a nemi magani,anan nake cewa iyaye su kara sa ido a kan'ya'yayansu mata su dungu tuntubarsu sunafahimtar da su tun kafin lokacin ya yidomin kada lokaci ya yi yarinya ta ga jinita fashe da kuka, ko makamantan haka,wata babbar mace ce amma bata sanmenene jinin al'ada ba ita dai kawai ta cetana ganin jini a wani lokaci bayan wasukwanaki kuma sai ta daina ganinshi.

  1. Wacce Ta Saba' Abinda ake nufi da

wacce ta saba ita ce wacce ta gabatar daal'ada sau uku a adadin kwanaki guda,misali wacce ta yi al'adar farko a kwanakibiyar, da ta sake yi sai ya yi mata kwanakibiyar da ta yi na uku shi ma kwanaki biyar,to wannan sai muce sunanta wacce tasaba domin ta saba akan kwanaki sanannu. Amma idan ta yi al'adar karo na farkokwanaki uku karo na biyu kuma kwanakibiyar karo na uku kwanaki shida to ba za'akira wannan wacce ta saba ba, domin bata da tsayayyun kwanaki.[6]Ita wacce ta saba wato wacce take dasanannun kwanakin al'ada to wadannankwanakin su ne kwanakin al'adarta, idankwanakin suka cika al'adar kuma ta daukesai ta yi wanka ta ci gaba da gudanar daibada da kuma sauran mu'amaloli na zamantakewar ma'aurata, amma idan kwanakin suka cikaal'adar kuma bata daukeba sai ta karakwanaki uku, haka zata dinga kara kwanakiuku har kwanaki shabiyar su cika, misaliidan al'adarta kwanaki biyarne sai kumajinin bai daukeba a kwanaki biyar din ba sai takara kwanaki uku na sauraron daukewarsun zama takwas kenan, idan ya daukeshi kenan sai wanka, idan kuma bai daukeba sai ta kara uku akan wadancantakwasdin sun zama sha-daya idan baidaukeba sai ta kara uku sun zama sha hudu idan bai daukeba sai ta kara kwanadaya, ya zama goma sha-biyar kenan, saita yi wankan kammala al'ada ko ya daukeko bai daukeba domin kwanakin al'adamakurarsu shi ne kwana goma sha-biyarkuma sun cika, abin da ya ci gaba da zuwaba sunan shi jinin al'ada ba sunanshi jinin cuta(Istihadha) sai a nemi magani, dukkanin wadancan kare-karen kwanakida aka yi inda ace bayan ta Kara kwanauku na saurare sai ya dauke a kwana nadaya cinkin ukun shi kenan sai ta yiwankan tsarki.Mu sani kamar yadda bayani ya gabatashi jinin al'ada bai wuce kwanaki goma sha-biyar ga wacce ta fara da wacce ta saba.

  1. Mai Juna-biyu (Mai ciki) Galibin mata

masu juna biyu basa al'ada, sabo da hakada zarar mace tana da juna biyu (ciki) saikuma ta ga al'ada to kada ta yi sakaciwurin tuntubar likita .Idan al'ada ta zowa mace mai junabiyu toidan cikin ya kai watanni uku zuwa biyar zataiya yin al'ada ta kwanaki sha-biyar zuwaashirin, idan kuma cikin ya kai watannishida to al'adar zata iya daukar kwanakiashirin zuwa ashirin da biyar, kada asha'afa wurin tuntubar likita idan ana dajuna biyu kuma aka ga jini.Tanbihi Na Daya: Idan mace jini yanamata wasa wato ya zo yau gobe sai kumaya dauke bayan kwanaki uku sai kuma yadawo to abinda zata yi anan shi ne, tatsaya ta yi karatun ta natsu, sai ta lissafakwanakin da jinin ya zo sune kwanakinal'ada sai kuma ta ware kwanakin da jininbai zoba sune kwanakin tsarki domin dahakane zata cika kwanakinta na al'ada,misali kwanaki tara; sai ya zo a rana tafarko da ta biyu sai bai zoba a rana ta ukuda ta hudu sai ya zo rana ta biyar ammabai zo ba a ta shida da ta bakwai sai yazo a ta takwas da ta tara. To anan saimuce ta yi al'adar kwana biyar a cikinkwanaki goma, wannan matar ita ake kira(Al-Mulaffiqa) alarabcin mata masu al'ada.Idan ya zama an sami tazarar kwanakitakwas ko sha-biyar tsakanin daukewarsada dawowarsa to na biyun zai zama sabonjini ne kenan, ba na da ne ya dawo ba.Alamar Daukewar Jinin Al'ada: idan jininal'ada ya dauke akwai alama da shara'a tasanya domin ya zama shi ne manuniya akancewar al'adarki ta dauke, wadannan alamusun kasu gida biyu kuma kowacce tana cingashin kantane, sune kamar haka:

  1. Bushewar Gaba: Abinda ake nufi anan

shine mace ta shigar da kyalle ko audugacikin gabanta ta fito da shi busasshe bawani jini a tare da shi, to da zarar ta gahaka to ta tabbata al'adarta ta dauke.

  1. Farar Kumfa: wannan wani ruwane fari

mai laushi da yake zuwa karshan al'ada,idan mace ta ga irin haka a karshanal'adarta to ta sani ta kammala.Wadannan alamomi su suke nunadaukewar al'adar mace, idan mace batataba ganin al'adaba sai a wannan karon saita fara ganin bushewar gaba to kai-tsayeta samu tsarki ba sai ta jira farar kumfa ba,amma idan wacce ta saba gani ce sai ta gabushewar gaba to malamai sukace zatazata dan saurara kadan domin jirar farankumfa, amma jinkirin ba zai kai ga fitarzababban lokacin sallah ba.A dunkule dai kowanne daya daga cikinwadannan abubuwa guda biyu yana nunasamuwar tsarki ba lalle sai sun hadualokaci guda ba, da zarar alamar ganintsarki ta tabbata sai ta yi wankan tsarkidomin ta ci gaba da ibada, domin idanbata yi wankaba ko da jinin ya daukemijinta ba zai sadu da ita ba kuma ba zatayi sallah ba, da dai sauransu.Idan mace ta ga ruwa fatsi-fatsi kodiddiga-diddiga bayan daukewar jininal'ada to kada ta damu ta ci gaba daharkokinta na ibada, dama matsalar idan taganshi a farkon jini ne, amma idan akarshen jini ne to wannan ba komai, UmmuAtiyyah medakin ma'aikin Allah (Tsira daamincin Allah su kara tabbata a gareshi) tace:((Mun kasance bama lissafa (Ruwa) fatsi-fatsi da diddiga-diddiga bayan tsarki dacewa wani abu ne)). Abu Daud Hadisi Na:307, Nasa'i, Hadisi Na: 368, Ibnu MajahHadisi Na: 647, Darimi Hadisi Na: 865.Mace ta dinga duba samun tsarkinta alokacin da zata kwanta bacci da kumalokacin sallar asuba, amma ba a ce ta tashicikin dareba domin ta duba.Idan mai al'ada ko mai biki (jinin haihuwa)ta ga tsarki kafin rana ta fadi to sallarazahar da la'asar sun hau kanta, hakanankuma idan ta ga tsarki kafin hudowar alfijito tabbas za ta yi sallar magariba da lisha.Abubuwan Da Basu Halatta Ga Mai-al'adaba:Anan za'a lissafa abubuwan da basuhalatta mai al'ada ta yi su ba ko ayi mataba, wadannan abubuwane guda goma:


1. Sallah: Bai halatta mai al'ada ta yisallaba farilla ko nafila, idan kuma tayi ta yiba'akarba ba sannan kuma ta yi laifi,sannan bayan ta kammala al'adar ba zatarama sallolinba.


2. Saki: Baya halatta matar da takeal'ada a saketa, wannan ya sabawakarantarwar musulunci, saboda haka kodayana son ya saketa to ya bari sai takammala al'ada kafin ya sadu da ita sai yasaketa, kuma dai idan ya saketa tana jininal'adar to sakin ya yi amma za'a tilasta shiya mayar da ita idan sakin bai kai ukuba.


3. Dawafi: Bai halatta mai al'ada ta yidawafin Ka'abah, amma zata yi saurandukkan abinda maniyyaci yake yi, kamartsaiwar Arafah da kwanan mina danamuzdalifa da jifa da Labbaika, da daidaisauransu.


4. Zama A Masallaci: mai al'adah ba zatazauna a cikin masallaciba, domin sauraronkaratu ko karantarwa ko taro da daisauransu.


5. Azumi: Bai halatta mai al'ada ta yiazumi na farilla ko na nafila, idan ta yi kumabai yiba, saboda haka zata lissafa azuminda ta sha bayan watan ya wuce sai taramasu. Ba'a ajiye azumi domin tsammaningobe al'ada zata zo, amma dazaran ta zoto dazaran ba azumi, dazaran bata zoba todazaran akwai azumi, ko da kin ji tafiyarjinin ajiki amma bai fitoba to biki faraal'adaba, sai ya fitane za'a fara lissafi.


6. Daukaa Alkur'ani: mai al'ada bata dauka Alqur'anikasantuwarsa littafi mai tsarki sannan kumaita bata da tsarki, amma wannan bayahana idan ta ganshi zai fadi ta daukeshi tagyara masa wuri.


7. Karatun Alkur'ani: mai al'ada batakaranta Alkur'ani, dudda cewa wadansumalamai suna ganin ya halatta takarantashi da ka domin kada ta mantasabanin dauka.


8. Saduwa: Bai halattaba saduwa damace tana al'ada, idan ta ki yadda damijinta ya sadu da ita domin tana al'adaba za'ace ta sabawa Allah ba asalima ta yibiyayyane ga reshi, bai halatta a sadu damace tana al'adaba har sai al'adar tadauke kuma ta yi wankan tsarki, kenankoda al'adar ta dauke amma batayiwankaba to bai halatta a sadu da itaba. Yahalatta miji ya taba duk inda yake so ajikin matarsa alokacin da take al'ada bayanta yi kunzugu inbanda daga cikbiyartazugwiwarta wannan kan bai halattaba harsai jinin ya dauke kuma tayi wanka,hakanan itama ya halatta ta taba ko ina ajikinsa duk da tana al'ada.


9. Tabbatar Da Rashin Tsarki: Al'adatana tabbatar da wacce take da ita batada tsarki.


10. Wajabta Wanka: Al'ada tana wajabtawanka, wato dukkan matar da ta yi al'adakuma al'adar ta dauke to wankan tsarki yawajaba akanta. Daga wadannan bayanan dasuka gabata ya bayyana a fili cewa lallejinin al'ada bakaramin hukunce-hukunceyake da shi ba, kuma lalle idan aka kyalleshiyadda ake sakaci tsakanin maza da mataakan abinda ya shafi wannan al'amari tolalle abin yanada ban tsoro.

Allah ya datar damu yasa mu dace. Allah shine mafi sanin masu sani.

Manazarta

🔥 Top keywords: