Khuraira Musa

Khuraira Musa Ƴar Najeriya ce, mazauniyar Amurka, ita shahararriyar kuma kwararriyar mai-kwalliya ce, shafe-shafe da kuma taimakon al'umma,[1] itace wacce ta zama shugaba ce ta kamfanin Khuraira kayan kwalliya. Khuraira ta shahara a fagen kwalliya da shafe-shafe na duniya, wanda kuma ta kasance tana gudanar da ajujuwan koyarwa ga mutane daga duniya baki daya. A rayuwar ta tayi kwalliya ga shahararrun mutane kamar su, Brandy, Mandy Moore, Paula Abdul, Kirstie Alley, Natalie Cole, Cher, Suzanne Douglas, Trista Rehn da kuma Dr. Suzanne Rice.[2]

Khuraira Musa
Rayuwa
HaihuwaLere
Sana'a
Sana'aMasu kirkira da ɗan kasuwa

Farkon rayuwa da aiki

Khuraira Musa an kuma haife ta a Ƙaramar hukumar Lere Jihar Kaduna, Najeriya. Ta rasa mahaifiyar ta a lokacin haihuwar ta, wanda hakan ne yasa ta rayu a gidan rainon marayu dake yankin Rukuba/Bassa a Jihar Plateau, amma bayan nan ta koma jihar Kaduna har sai da ta kammala makarantar sakandare.[1] A shekarar 1992 taje kwaleji a Tarayyar Amurka wanda anan ne ta fara aiki a shaguna. [3][2]

Ta kuma fara harkan kwalliya a shekarar 2004 sannan tayi shekara 23 a kan wannan harka na kwalliya[4]

Aikin agaji

Khuraira Musa ta kafa gidauniyar da ake kira da suna Arewa Development Support Initiative (ADSI) hukuma wacce bata gwamnati ba, da niyyar taimakawa cigaban matasa da mata a yankin Arewacin Najeriya.[5][6][7] Gidauniyar na tallafawa da samun karatu ga mata, sana'o'in hannu da dabarun kasuwanci. Khuraira itace ta samar da makarantar Zainab Memorial saboda karantar da marasa karfi musamman marayu waɗanda ke a Bassa/Rukuba a Jihar Plateau.[8][9]

Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.


Manazarta

Hanyoyi haɗi na waje