Tsibirin Bamuda

Tsibirin Bamuda Duk da [1] cewa a duniya abubuwan mamaki dake faruwa a cikinsu ba tareda Dan Adam ya fahimci musabbabansu ba,Tsibirin Bamuda (Bermuda Island ko BermudaTriangle) ne kadai ya fi shahara a bakunanmutane sanadiyyar haka. Wannan shahara tasamo asali ne daga nahiyar Amurka(South America), a hankali labarin ya ci gaba dayaduwa zuwa sauran kasashen duniya. Manyanababen mamakin da ake ikirarin suna faruwa amuhallin tekun da wannan tsibiri yake sun hadada bacewar jiragen sama – masu dauke dafasinjoji dan kasuwa ko na soji – da jiragenruwa – manya da kanana da na shawagi. Idansuka bace a galibin lokuta, ba a ganin buraguzanjirgin balle a kaddamar da bincike kan dalilan dasuka haddasa faruwar hadarin. Wannanal’amaran ababen al’ajabi ne. A cewar masu bayar dalabarai, bai tsaya a bacewar jirage ba tare daganin buraguzansu kadai ba, har da wasulabarai masu ruda kwakwalwa kan irin yanayinda tekun ke kasancewa na launi da kumasulmuya a wasu lokutan, ko kuma wasu irindabi’u da ake ikirarin gira-gizan da ke samanteku ke shiga, a yayin aukuwar hadarurrukanda suka fara faruwa shekaru kusan dari biyu dasuka gabata. Ire-iren wadannan labarai sunsamo asali ne daga irin jawaban da masu lura dana’urar filin saukan jiragen sama da ke tsibirin kebayarwa. Ko wadanda ake tarawa wajenbinciken da hukumomin gwamnatin Amurka dake lura da ire-iren wadannan hadarurruka ke yi.Da wannan, marubuta suka sa wa wannanmuhalli suna: The Bermuda Triangle (KusurwarBamuda), ko kuma The Devil’s Triangle(Kusurwar Shedan).A halin yanzu da dama cikin wadanda suka tabajin labarin wannan bigire na Bamuda, sun yardacewa wani wuri ne mai cike da almara, kamaryadda galibin turawa masu bincike suka fada.Da kuma cewa babu wanda ya san abin da kehaddasa wannan al’amari, sai Allah (gawadanda suka yarda da Allah kenan), ko kumadabi’a ta shu’umcin wurin. Wasu suka ce aljanune a wurin. Wasu suka ce akwai wasu halittu nena musamman da a harshen Turanci ake kiraAliens, masu haddasa hakan. Wasu suka ce a'a,irin yanayin wurin ne kawai. Da dai sauranra’ayoyi masu kama da haka. Shin, meyegaskiyar wadannan zantuttuka da ake ta yi kanwannan tsibiri? Wani irin bincike aka yi wajengano hakan? Jiragen ruwa da na sama gudanawa suka bace a wannan mahalli? Rayukanawa suka salwanta? Wa da wa suka yi rubuce-rubuce kan haka cikin Malam Kimiya da masusha’awar rubutu kan al’amuran mamaki aduniya? Meye ra’ayin nazarin da MalamanKimiyya suka yi kan dalilin faruwar wadannanabubuwan mamaki? Shin, wai ma tukun, aduniya akwai wasu wurare ne masu irin wannandabi’a, ko dai tsibirin Bamuda ne kadai? In ehakwai, to me ya sa na tsibirin Bamuda ya shabamban, ya shahara fiye da sauran a duniya?Wadannan, da ma wasu tambayoyi, za mu samuamsoshinsu cikin makonni masu zuwa in AllahYa yarda.A Ina Tsibirin Yake?Kafin mu yi nisa, asalin tsibirin Bamuda, watauBermuda Islands, yana gab da tsakiyar tekunAtlantika ne, Arewa da Jihar Fulorida da keAmurka. Kuma duk da cewa ana dangantawannan wuri ko kusurwa da tsibirin Bamuda, saidai ba a wannan tsibiri kadai wannan kusurwayake ba. Kusurwar Bamuda wani wuri ne da yahada manyan gabar tekunan kasashe guda ukuda ke nahiyar Arewaci da kuma kudancinAmurka. Kusurwar farko ta faro ne daga gabarFulorida ta kasar Amurka, ta zarce zuwa gabarbabban tsibirin Puerto Rico da ke yamma maso-kudu da gabar Fulorida. Daga tsibirin PuertoRico kuma kusurwar ta cilla Arewa, inda ta tike agabar tsibirin Bamuda da ke kusa da tsakiyartekun Atlantika. Wannan wuri ko mahalllin tekuda ke tsakanin wadannan gabobi guda uku, shiake kira The Bermuda Triangle, ko The Debil’sTriangle.An danganta wannan kusurwa da tsibirinBamuda ne saboda a nan ya tike, kuma galibinababen hawa kamar su jiragen sama da na ruwawadanda ake amfani da su wajen kasuwanci dashawagi da atisayen soji a wannan nahiya, duk acan suke tikewa kafin su komo inda suka taso.Ko kuma daga can suke wucewa zuwa wasunahiyoyin, irin su Turai da Arewacin Amurka dakasashen Asiya.Wannan kusurwa ta Bamuda ita ce bigiren dajiragen sama da na ruwa ke shawagi fiye dakowane wuri a duniya. An kiyasta cewa akallaakan samu sawun jiragen sama daga wannannahiya zuwa kasashen turai da sauran nahiyoyi,sama da dubu hamsin a shekara. Bayan haka,akwai jiragen ruwa da na kasuwanci da nashawagi ko yawon bude ido, da kuma jiragensaman atisayen soji da Hukumar Sojin Amurkake turawa suna shawagi, watau kai-komo donyin atisaye. Har wa yau akwai masu shawagi dakananan kwale-kwalen shakatawa wadanda aharshen turanci ake kira Pleasure Boats, dakuma jiragen ruwan tsere da ake kira Yatchers.Bayan haka, akwai filayen saukan jiragen sama adukkan kusurwoyin nan uku, tare da tasharjiragen ruwa masu karban manya da kanananjiragen da ke shawagi a wannan wuri. Sannankuma sai miliyoyin masu zuwa yawon bude idodaga sauran kasashen duniya, musamman maAmurka da Turai. A takaice dai, wannan wurirayayyen wuri ne da sawun jirgin ruwa da nasama da na masu ziyara ba su daukewa; dagashekara zuwa shekara.Zai dace mai karatu ya rike wannan karatu kanyawan zirga-zirgar da ake yi a wannan wuri,domin zai taimaka masa wajen karba ko rashinkarbar dalilan da wasu marubuta suka bayarwajen yanke hukuncinsu na karshe.Yaushe Abin Ya Fara?Wannan kusurwa da ake wa take da “KusurwarShedan” – ko Debil’s Triangle – ya fara cinjiragen sama da na ruwa ne shekaru kusan daribiyu da suka gabata, duk da cewa ba a farafahimtar hakan ba sai wajen shekaru casa’inzuwa dari da suka wuce.

Tsibirin Bermuda
urban legend (en) Fassara, yankin taswira da triangle (en) Fassara
Bayanai
Suna sabodaBermuda
ƘasaBirtaniya, Bahamas da Tarayyar Amurka
Ƙasantuwa a yanayin ƙasaTekun Atalanta
Gagarumin taron1948 Airborne Transport DC-3 (DST) disappearance (en) Fassara
Shape (en) Fassaratriangle (en) Fassara
Wuri
Map
 25°N 71°W / 25°N 71°W / 25; -71


Bermuda_Triangle_with_Corkscrew_in_the_background

Bermuda triangle
Wannan taswirar tsibirin bermuda kenan.
bermuda
Wannan wani sashi ne daga tsibirin bermuda.

Daga nan ne aka faradanganta hadarurrukan da suka gabata dawannan yanayi mai ban mamaki. Kamar yaddabayanai suka gabata, wannan kusurwa taBamuda ta yi kaurin suna ne wajen hadararrukamasu ban mamaki, inda bayan hadarin ake rasaabin da ya haddasa shi, ko kuma a ma kasasamun buraguzai ko gawawwakin wadanda sukarasa rayukansu da ma na jirgin gaba daya.A wasu lokuta a kan samu sakon neman agajidaga direbobin jiragen sama cewa suna ganinwasu abubuwa masu ban tsoro ko firgitarwa.Kafin a mayar da jawabin ceto garesu, sai kawaia nemi hanyar sadarwa a rasa. Wani kuma zaibugo ne cewa ba ya ganin gabansa, bayan kumaa na’urar lura da yanayin sararin samaniya babuwata matsala da na’urar ke hangowa: babuyanayin hazo mai firgitarwa, babu ruwan sama,babu alamar mahaukaciyar guguwa mai yi wajiragen ruwa dibar karan mahaukaciya, ammasai kawai a ji hanyar sadarwar ta yanke.Mafi shahara daga cikin abubuwan mamaki dasuka faru a wannan kusurwa shi ne hadarintawagan jiragen kai hari da darkake abokan gabana kasar Amurka masu suna Flight 19, wadandahukumar sojin sama na kasar Amurka ta aikadon yin shawagi a wannan kusurwa cikinshekarar 1945. Duk da cewa ana lura da tafiyarwannan tawaga na jirage ta hanyar na’urahangen nesa sadda suka baro cikin kasarAmurka, sai dai cikin lokaci guda kawai sai akaneme su aka rasa. Da aka nemi sadarwa dashugaban tawagar, sai ya ce: “A yanzu munashiga wani irin farin ruwa ne...al’amura sun faralalacewa. Bamu san inda muke ba a halinyanzu...ruwan kore ne...a a, fari ne!”, saisadarwa ta yanke a tsakanin masu lura dana’urar da wannan shugaban tawaga.Bayan faruwar wannan lamari, an yi ta bincikecikin teku ba a samu buraguzan wadannanjirage ba balle wadanda suke ciki. Babu wandake da wani bayani gamsasshe kan abin da yahaddasa wannan hadari har zuwa yau, ballebayani kan hakikanin wurin da abin ya auku. Alokacin da aka tura wata tawaga ta manemajirage, da suka isa wurin da na’urar ta sanar dafaduwarsu, babu abin da aka gani a wurin.Daga nan aka ci gaba da samun ire-irenwadannan hadarurruka masu ban mamaki daal’ajabi. Wasu a kan samu bayanai kan batansu,bayan tsawon lokaci; wasu kuma ko alama ba asamu, sai dai kawai a hakura,bamuda dai takasance waje ne dake tsakiyan ruwa wanda malamai da dama suka bayyana banda ubangiji bawanda yasan menene yake cikin tsibirin bamuda dai malamai sunce kaman malam muhammad Auwal Adam wanda akafi sani da albani yace banda al-arshin allah madaukakakin sarki babu wani waje ko kuma wani masarauta da tafi tafkin tekun bamuda tsaro a duniya gaba daya.

Manazarta


🔥 Top keywords: