Uzamat Akinbile Yussuf

Uzamat Akinbile Yussuf wacce aka fi sani da Uzamat Folashayo Akinbile Yussuf (an haife ta a shekara ta 1976),[1] Ita mai harhaɗa magunguna ce (pharmacist), mai kare hakkin matasa, ’yar siyasa, kuma mai son taimakon al'umma.[2] Ita ce kwamishina a yanzu haka a Ma’aikatar Yawon Buɗe Ido ta Jihar Legas, an canza matsayinta daga Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida na Jihar Legas zuwa ta Ma'aikatar bude ido (Torism) na Jihar Legas.[3][4][5]

Uzamat Akinbile Yussuf
Rayuwa
Haihuwa1976 (47/48 shekaru)
ƙasaNajeriya
Karatu
MakarantaJami'ar Lagos 2006)
Sana'a
Sana'aɗan siyasa

Ilimi

Ta halarci makarantar firamare ta Ansar-ud-deen Primary School, Ile ife a tsakanin shekarar 1980 zuwa 1986. Daga baya, ta sami shiga cikin makarantar Seventh Day Adventist Grammar, Ile Ife tsakanin 1987 da 1992. Ta samu shiga Jami’ar Lagos, inda ta kammala a shekara ta 2006.[2] Ta kasance memba na kungiyar masu hada Magungunanwato Association of Ladies Pharmacists Society (ALPS), da kuma kungiyar Social Workers of Nigeria (NASOW) da kuma kungiyar Pharmacists Society of Nigeria.[3] Ta buga wani littafi mai suna Duty Calls.[3][6]

Rayuwar mutum

Tana da aure da yara.

Manazarta