Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya, Bauchi
Tools
General
Fitar/kaiwa waje
Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya, Bauchi | |
---|---|
Bayanai | |
Suna a hukumance | Federal Polytechnic, Bauchi |
Iri | polytechnic (en) |
Ƙasa | Najeriya |
Harshen amfani | Turanci |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 1979 |
fptb.edu.ng |
Kwaalejin Kimiyya da Fasaha, Bauchi ɗaya daga manyan makarantu ne dake garin Bauchi, wanda ya kasance gari na hedikwatar masarautar gargajiya kana kuma babban birnin jihar Bauchi, dake Arewa maso Gabashin Najeriya.
An kafa Kwalejin Fasaha ta Tarayya ta Bauchi a watan Yulin shekarata 1979 ta hanyar Dokar 33 (Decree 33) na Tarayyar Najeriya tare da wasu cibiyoyin har guda shida tare da izinin gudanar da karatu na cikakken lokaci da / ko kuma rabin lokaci akan darussan fannoni na Fasaha, Ilimin Kimiyya, Kasuwanci, Gudanarwa da sauran wasu fannonin da suka dace don buƙatar ci gaban Nijeriya. Tana nan a ƙauyen Gwallameji, hanyar Bauchi - Dass. Shugaban makarantar na yanzu shi ne Arch. Sanusi Waziri Gumau. Tsangayoyin da ke bayar da karatun da za su kai ga kyautar difloma ta kasa da babbar difloma na makarantar sun samu amincewa don gudanar da kwasa-kwasan digiri tara a shekarar 2020 da hadin gwiwar Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa, Bauchi.
A makarantar a na koyar da waɗannan kwasa-kwasan;