Sainey Njie

Kwararen Dan wasan kwallon kafa ne a Gambia

Sainey Njie,(an haife shi a ranar 30 ga watan Agusta 2001) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne ɗan ƙasar Gambia wanda ke taka, leda a Zemplín Michalovce yana fafatawa a Fortuna Liga a matsayin ɗan wasan tsakiya, da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Gambia.

Sainey Njie
Rayuwa
HaihuwaLamin, Western Division, Gambia (en) Fassara, 30 ga Augusta, 2001 (22 shekaru)
ƙasaGambiya
Sana'a
Sana'aɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
ƘungiyoyiShekaruWasanni da ya/ta bugaƘwallaye
FC DAC 1904 Dunajská Streda (en) Fassara-
 
Muƙami ko ƙwarewaMai buga tsakiya
Tsayi182 cm

Aikin kulob

Njie ya buga wasansa na farko na Fortuna Liga a DAC Dunajská Streda a wasan waje da Spartak Trnava a ranar 21 ga watan Yuni 2020. Ya, shigo a wasan a mintunan karshe ya maye gurbin Eric Ramírez. DAC ta lashe wasan da ci 2-0.[1] [2] A wasa mai zuwa ya yi ya kasance acikin sha dayan da zakarar Slovan Bratislava, tare da DAC daci 3-1 a MOL Aréna. Andrej Fábry ne ya maye gurbin Njie bayan sama da mintuna 70, a kokarin da ya yi na zura kwallo a raga. [3]

A lokacin kakar 2020-21, Njie ya buga wa Šamorín wasa yayin da kuma yake fitowa a Dunajská Streda, a matsayin 2. Kulob ɗin Liga ƙungiyar 'farm' ce ta DAC.[4]

Ayyukan kasa da kasa

Njie ya fafata a Gambia a wasan sada zumunci da suka doke Congo da ci 1-0 a ranar 9 ga watan Oktoba 2020.[5]

Manazarta

Hanyoyin haɗi na waje