The Road of Hope (fim)
Tools
General
Fitar/kaiwa waje
The Road of Hope (fim) | |
---|---|
Asali | |
Lokacin bugawa | 1957 |
Asalin suna | طريق الأمل |
Asalin harshe | Larabci |
Ƙasar asali | Misra |
Characteristics | |
Genre (en) ![]() | romance film (en) ![]() |
During | 105 Dakika |
Direction and screenplay | |
Darekta | Ezz El-Dine Zulficar |
'yan wasa | |
Samar | |
Mai tsarawa | Helmy Rafla |
External links | |
Specialized websites
|
Tareeq al-Amal ( Larabci: طريق الأمل , The Road of Hope ) wani fim ne na soyayya / wasan kwaikwayo na Masar a shekara ta 1957 wanda darektan fina-finan Masar Ezz El-Dine Zulficar ya bada Umarni. [1] Cikin shirin akwai Rushdy Abaza,[2] Shukry Sarhan, da Faten Hamama.
Saneya ( Faten Hamama ) wata budurwa ce mahaifiyarta tana fama da wani mugun cuta wanda ya hana ta yin aiki. Wannan ya sa ita da mahaifiyarta ba su da kuɗi, hakan ya tilasta mata yin karuwanci . Wata rana ta haɗu da wani Husaini ( Shukry Sarhan ) wanda ya tausayawa halin da take ciki kuma ya yanke shawarar ceto ta daga wannan mummunan aiki. Yana sonta ya yanke shawarar aurenta, amma mahaifiyarsa ( Ulweya Gameel ) ba ta yarda da shi ba saboda ita ta san wacece kanta. Saneeya ta koma aikin karuwanci. Wata rana, ta ceci ƴar'uwar masoyinta ( Zahret El-Ula ) wanda ya shawo kan mahaifiyarsa wanda ya yarda da ita a matsayin matar danta.