Al Farabi

Abu Nasr Muhammad Al Farabi (Arabic: أبو نصر محمد الفارابي), wanda aka fi sani a kasashen yamma da Alpharabius;[1](C.870[2]- tsakanin 14 ga Disamba, 950 da 12 ga Janairu, 951)[3] sananne ne daga cikin malaman Musulunci na farko na falsafa kuma masanin alkalanci kuma yayi rubututtuka a fannin falsafar siyasa, da kuma ilimin dake magana akan wanzuwa, kyawawan dabi'u da kuma nazari a kimiyyance. Kuma masanin kimiyya ne, kuma masani ne akan nazarin falaki, masanin lissafi ne, music theorist kuma masani akan magunguna.[4]

Al Farabi
Rayuwa
HaihuwaOtrar (en) Fassara, 870
ƙasaDaular Abbasiyyah
Harshen uwaTurkanci
MutuwaDamascus, 950
Karatu
HarsunaLarabci
Farisawa
Sogdian (en) Fassara
MalamaiAbu Bishr Matta ibn Yunus (en) Fassara
Yuhanna ibn Haylan (en) Fassara
Muhammad ibn al-Sari ibn al-Sarraj (en) Fassara
Ɗalibai
Sana'a
Sana'amai falsafa, physicist (en) Fassara da music theorist (en) Fassara
Muhimman ayyukaAra Ahl al Madina al Fadila (en) Fassara
message in the mind (en) Fassara
Alfarabi's Philosophy of Plato and Aristotle (en) Fassara
Kitab al-Musiqa al-Kabir (en) Fassara
Wanda ya ja hankalinsaAristotle, Plato da Plotinus (en) Fassara
Imani
AddiniMusulunci

Tarihi rayuwa

Mganganu akan tarihin al-Frabi bawai an samo su bane lokacin rayuwarsa ko bayan bai dade da rasuwa ba ga wadanda suke da hujjoji, amma an samesu ne a bakunan mutane da kuma canke-canke. Abubuwa kadan aka sani a kanshi.[5]Daga abubuwan da aka san faru an san cewa yayi zauna a Bagadaza mafi yawan rayuwarsa tare da malaman addinin kiristaci na Siriya daga cikinsu akwai Yuhanna ibn Haylan, Yahya ibn Adi da Abu Ishaq al Baghdadi. Daga baya kuma ya zauna a Damaskas da kuma Misra kafina Damaskas a inda ya mutu a shekarar 950-951.[6]

Addini

Akidar da AL-Farabi yake bi a cikin musulunci har yanzu ana gaddama akan akidar shi. Wasu masanar tarihi sunce dan akidar Sunni,[7] wasu kuma sunce dan Shi'a ne ko kuma ya tasirantu da akidar Shi'a.

Aiki da Gudummuwa

Al-Farabi ya bada gudummuwa a bangarorin Nazari, Lissafi, Kida, falsafa, sanayyar halayen dan adam da kuma ilimi.

Manazarta

🔥 Top keywords: