Ondo (jiha)

Jiha ce a Najeriya

Jihar Ondo Jiha ce dake kudu maso yammacin Najeriya. An ƙirƙiri jihar Ondo a ranar 3 ga watan Fabrairun shekara ta 1976 daga tsohuwar yankin Yammacin Najeriya.[1] Ondo na da iyaka da jihar Ekiti (wanda a da tana cikin jihar Ondo ne) daga arewa, Jihar Kogi daga arewa maso gabas, jihar Edo daga gabas, Delta daga kudu maso gabas, Ogun daga kudu maso yamma sannan kuma jihar Osun daga arewa maso yamma sai kuma Tekun Atlantic daga kudu. Babban birnin jihar shi ne Akure, babban birnin masarautar Akure a da.[2] Ondo na da kasafin daji na mangrove-swamp forest kusa da gaɓar Benin.[3]

Ondo


Wuri
Map
 7°10′N 5°05′E / 7.17°N 5.08°E / 7.17; 5.08
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya

Babban birniAkure
Yawan mutane
Faɗi4,671,695 (2016)
• Yawan mutane301.4 mazaunan/km²
Harshen gwamnatiTuranci
Labarin ƙasa
Yawan fili15,500 km²
Sun raba iyaka da
Bayanan tarihi
MabiyiJihar Yammacin Najeriya
Ƙirƙira3 ga Faburairu, 1976
Tsarin Siyasa
Majalisar zartarwaexecutive council of Ondo State (en) Fassara
Gangar majalisaMajalisar dokokin jihar Ondo
Bayanan Tuntuɓa
Lambar aika saƙo340001
Kasancewa a yanki na lokaci
Lamba ta ISO 3166-2NG-ON
Wasu abun

Yanar gizoondostate.gov.ng
mutanen ondo
Gajeren zance na tarihin Ondo cikin yaren Ondo daga ɗan asali harshen
kasuwa a ondo

Ana mata laƙabi da "Sunshine State" wato "jiha mai haskakawa". Jihar Ondo ita ce ta tara a girma a Najeriya.[4] Kuma ita ce jiha ta 25 a faɗin ƙasa.[5] Mafi akasarin mutanen garin yarbawa ne.[6][7] Akasarin mutanen garin yarbawa ne, a yayinda ake amfani da harshen yarbanci a garin. Albarkatun ƙasan Ondo ya ta'allaka ne a kan man fetur, noman cocoa, da makamantansu.[8] Inda tsaunukan Idenre suke, wanda shi ne tsauni mafi girma a yankin yammacin Najeriya.

daya daga cikin manyan makarantu na jihar ondo


Tana da yawan fili kimanin kilomita murabba’in 15,500 da yawan jama’a miliyan uku da dubu dari huɗu da arba'in (ƙidayar a shekara ta 2006). Babban birnin tarayyar jahar shi ne Akure. Oluwarotimi Odunayo Akeredolu, shi ne gwamnan jihar tun zaɓen shekara ta 2011 har zuwa yau. Mataimakin gwamnan shi ne Agboola Ajayi. Dattijan jihar su ne: Yele Omogunwa, Robert Ajayi Boroffice da Omotayo Donald.

Jihar Ondo tana da iyaka da jihohin shida: Delta, Edo, Ekiti, Kogi, Ogun kuma da Osun.

Gwamnati

Akeredolu Oluwarotimi Odunayo daga jam'iyyar APC ne gwamnan Jihar Ondo wanda aka rantsar a ranar 24 ga watan Fabrairun shekara ta 2017,[9] kuma ya karɓi mulkin daga hannun Olusegun Mimiko.[10] Mataimakinsa shi ne Lucky Aiyedatiwa.[11]

ondo

Kananan Hukumomi

Jihar Ondo nada adadin Kananan hukumomi guda goma sha takwas (18) sune:


Kididdigar Jama'a

Kididdiga akan yawan al'ummar jihar Ondo[12]
Local government areaMaleFemaleTotal
Akoko North-West108,057105,735213,792
Akoko North-East93,06082,349175,409
Akoko South-East41,99540,43182,426
Akoko South-West123,979105,507229,486
Ose73,39571,506144,901
Owo110,429108,457218,886
Akure North66,87864,709131,587
Akure South175,495177,716353,211
Ifedore92,01484,313176,327
Ile Oluji87,50585,365172,870
Ondo West139,400144,272283,672
Ondo East38,03236,72674,758
Idanre66,99662,028129,024
Odigbo114,814115,537230,351
Okitipupa120,626112,939233,565
Irele75,63669,530145,166
Ese Odo78,10076,878154,978
Ilaje154,852135,763290,615
Total1,761,2631,679,7613,441,024

Manazarta


Jihohin Najeriya
Babban birnin tarayyar (Abuja) | Abiya | Adamawa | Akwa Ibom | Anambra | Bauchi | Bayelsa | Benue | Borno | Cross River | Delta | Ebonyi | Edo | Ekiti | Enugu | Gombe | Imo | Jigawa

Kaduna | Kano | Katsina | Kebbi | Kogi | Kwara | Lagos | Nasarawa | Neja | Ogun | Ondo | Osun | Oyo | Plateau | Rivers | Sokoto | Taraba | Yobe | Zamfara

🔥 Top keywords: