Nana Klutse

Nana Ama Browne Klutse tana nazarin canjin yanayi na Afirka ta Yamma. Aikinta yana mai da hankali ne kan kimiyyar yanayi da ci gaba musamman kan Damuwar kasashen Afirka.[1][2] Ita ce babbar malama a Sashin ilimin kimiyyar lissafi, Jami'ar Ghana. A baya, tana kula da Cibiyar hangen nesa da yanayi. Dokta Klutse masanin Kimiyyar Yanayi ce ta cibiyar Nazarin Lissafi ta Afirka kuma babban marubuciya CE dake ba da gudummawa ga Rahoton Bincike na shida na IPCC (AR6). Ta kuma karfafa gwiwa ga 'yan mata a kasar Ghana don yin la'akari da ayyukan kimiyya da kuma tallafawa ci gaban ilimin kimiyya a kasar.

Nana Klutse
Rayuwa
Haihuwa23 Mayu 1981 (42 shekaru)
ƙasaGhana
Karatu
MakarantaUniversity of Cape Town (en) Fassara
(13 ga Faburairu, 2007 - 9 Disamba 2012) Doctor of Philosophy (en) Fassara
Sana'a
Sana'aclimatologist (en) Fassara da researcher (en) Fassara
EmployersUniversity of Cape Coast  (1 Satumba 2004 -  1 ga Faburairu, 2011)
University of Cape Coast  (2 ga Faburairu, 2011 -  1 Oktoba 2011)
Ghana Atomic Energy Commission (en) Fassara  (1 Oktoba 2011 -  31 ga Yuli, 2018)
University of Ghana  (1 ga Augusta, 2018 -  31 ga Janairu, 2021)
African Institute for Mathematical Sciences Rwanda (en) Fassara  (1 ga Maris, 2020 -

Kwarewar sana'a

Nana Klutse

Dokta Klutse ta yi aiki a Cibiyar Kimiyyar Sararin Samaniya da Fasaha ta Ghana na Hukumar Kula da Makamashin Atom a matsayin babban masanin kimiyyar bincike daga shekara ta 2016 zuwa shekara ta 2018. Kafin wannan, ta kasance bakon malama a Cibiyar Bayar da Ilimin Kimiyyar Yammacin Afirka kan Yanayi da Ingantaccen Amfani da Kasa (WASCAL) da ke Akure, Kasar Najeriya.[3][4][5][6]

Siyasa

Nana Klutse

Dokta Klutse kuma tana aiki a cikin siyasa a matsayin memba na National Democratic Congress.

Manazarta