Abolhassan Banisadr

Abolhassan Banisadr Dan siyasar kasar Iran ne kuma marubuci. Shine shugaban kasar Iran na farko bayan an tabbatar da Gwamatin musulunci sakamakon juyin juya hali da akayi a shekarar 1979, ya kasance a wannan kujera ta shugaban kasa na wasu watanni daga shekara ta alif 1980 zuwa shekarar 1981. wanda daga bisani masu zartarwa na kasar suka tsigeshi daga mukamin na shugaban kasa. Kafin kasancewarshi shugaban kasa, shine minista mai kula da harkokin waje. Ya zauna kasar faransa a shekaru masu dama inda ya kirkiri wata kungiya a siyasan ce mai suna National Council of Resistance of Iran dake yaki da manufofin sabuwar Gwamnatin musulunci ta iran.

Abolhassan Banisadr
1. President of Iran (en) Fassara

5 ga Faburairu, 1980 - 22 ga Yuni, 1981
← no value - Mohammad-Ali Rajai
Minister of Economic Affairs and Finance (en) Fassara

17 Nuwamba, 1979 - 10 ga Faburairu, 1980
Ali Ardalan (en) Fassara - Hossein Namazi (en) Fassara
Foreign Affairs Minister of Iran (en) Fassara

12 Nuwamba, 1979 - 29 Nuwamba, 1979
Ebrahim Yazdi (en) Fassara - Sadegh Ghotbzadeh (en) Fassara
Rayuwa
HaihuwaHamadan (en) Fassara, 22 ga Maris, 1933
ƙasaPahlavi Iran (en) Fassara
Iran
MazauniVersailles (en) Fassara
Harshen uwaFarisawa
Mutuwa13th arrondissement of Paris (en) Fassara, 9 Oktoba 2021
Ƴan uwa
MahaifiNasrallah Banidsadr
Yara
AhaliFathullah Banisadr (en) Fassara
Karatu
MakarantaUniversity of Paris (en) Fassara
University of Tehran (en) Fassara
HarsunaFarisawa
Faransanci
Turanci
Sana'a
Sana'aɗan siyasa, Mai tattala arziki, ɗan jarida, essayist (en) Fassara da marubuci
Aikin soja
Fannin sojaArmed Forces of the Islamic Republic of Iran (en) Fassara
Digiricommander-in-chief (en) Fassara
Ya faɗaciIran–Iraq War (en) Fassara
Imani
AddiniMusulunci
Jam'iyar siyasano value
banisadr.org
Abolhassan_Banisadr_sign

Rayuwa da karatun shi

An haifi Banisadr a ranar 27 ga watan maris a shekarar 1933[1] kuma mahaifin shi ayatollah ne kuma makusanci ga Ruhollah Khomeini[2] Banisadr ya karanci ilimin shari,a tare da ilimin fahimtar halin dan adam a [[jami'ar Tehran]] [3] A shekarun 1960 ya karanci ilimin kudi da tattalin arziki a jami'ar Sorbonne[4][5] Mahaifin Banisadr ya rasu a shekarar 1972 wanda akayi jana'izarshi a kasar iraq kuma ya kasance lokaci na farko da Banisadr ya taba haduwa da Ayatollah Khomein[6] Banisadr ya kasance daya daga cikin kungiyar dalibai masu yaki da Gwamnatin Shah a farkon shekarun 1960 a sanadiyyar haka yaje gidan yari har sau biyu kuma ya samu mummunar rauni wanda hakan ya jaza masa tafiya kasar faransa, kuma gada bisani ya shiga kungiyar turjiya ga Gwamnatin iran wanda Ayatullah Khumaini ke jagoranta kuma ya kasance daya daga cikin manyan wannan kungiya[7][8] Banisadr ya dawo kasar Iran tare da Imam Khomaini a farkon juyin juya hali a watan fabairun shekarar 1979. Ya rubuta littafi mai huddatayyar kudi a musulunci mai suna Eghtesad Tohidi[9]

Manazarta

🔥 Top keywords: