Volodymyr Zelensky

Volodymyr Oleksandrovych Zelenskyy da Hausa ana furta sunan shi da Zelenskai an haife shi a ranar 25 ga watan Janairu shekara ta 1978. Ɗan ƙasar Ukraniya ne, tsohon ɗan wasan kwaikwayo kuma ɗan wasan barkwanci wanda shi ne shugaban ƙasa na shida kuma shi ne shugaban ƙasar Ukraniya na yanzu.[1][2]

Volodymyr Zelensky
Murya
6. President of Ukraine (en) Fassara

20 Mayu 2019 -
Petro Poroshenko (en) Fassara
Supreme Commander of the Armed Forces of Ukraine (en) Fassara

20 Mayu 2019 -
Rayuwa
HaihuwaKryvyi Rih (en) Fassara, 25 ga Janairu, 1978 (46 shekaru)
ƙasaUkraniya
Kungiyar Sobiyet
MazauniMariinskyi Palace (en) Fassara
ƘabilaUkrainian Jews (en) Fassara
Harshen uwaRashanci
Ƴan uwa
MahaifiOleksandr Zelenskyy
MahaifiyaRimma Zelenska
Abokiyar zamaOlena Zelenska (en) Fassara  (2003 -
Yara
Karatu
MakarantaKyiv National Economic University named after Vadym Hetman (en) Fassara
Kryvyi Rih Institute of Economics (en) Fassara
(1995 - 2000) : Doka
HarsunaRashanci
Harshan Ukraniya
Ibrananci
Turanci
Harshen Japan
Yaren Sifen
Faransanci
Sana'a
Sana'aɗan siyasa, cali-cali, mai gabatar wa, mai tsara fim, marubin wasannin kwaykwayo, Jarumi, mai tsare-tsaren gidan talabijin, mai gabatarwa a talabijin, entertainer (en) Fassara, mawaƙi, humorist (en) Fassara, filmmaker (en) Fassara, showman (en) Fassara, KVN actor (en) Fassara, soja da impressionist (en) Fassara
Tsayi167 cm
Wurin aikiKryvyi Rih (en) Fassara da Kiev
EmployersKvartal 95 (en) Fassara
1+1 (en) Fassara
Inter (en) Fassara
Office of the President of Ukraine (en) Fassara
Muhimman ayyukaServant of the People (en) Fassara
Kyaututtuka
Wanda ya ja hankalinsaAlexander Maslyakov (en) Fassara
Sunan mahaifiЗелёный
Artistic movementpolitical satire (en) Fassara
parody (en) Fassara
barkwanci
humor (en) Fassara
Kayan kidamurya
Aikin soja
Fannin sojaArmed Forces of Ukraine (en) Fassara
DigiriSoldat (rank) (en) Fassara
Ya faɗaciMamayewar Rasha na Ukraine na 2022
War in Donbas (en) Fassara
Imani
Jam'iyar siyasaServant of the People (en) Fassara
IMDbnm3305952
president.gov.ua da ze2019.com
Volodymyr Oleksandrovych Zelenskyy da ilham
Volodymyr Oleksandrovych Zelenskyy
Volodymyr Oleksandrovych Zelenskyy a majalisar dokokin kasar Koriya
Volodymyr Oleksandrovych Zelenskyy da gwamnan holan

Zelenskyy ya girma a Kryvyi Rih, babban birni a yankin da ake magana da harshen Ukraniya a tsakiyar Ukraniya. ya sami digiri a fannin shari'a daga Jami'ar Tattalin Arziƙi ta Kyiv. Daga nan sai ya fara wasan kwaikwayo shi ne wanda ya ƙirƙiro kamfanin Kvartal 95, wanda ke samar da fina-finai, zane-zane/kaatuun, da kuma watsa fina-finai na shows TV cikin finafinan shi akwai Servant of the People, wanda Zelenskyy ya fito a matsayin shugaban kasar Ukraniya. Film ɗin mai dogon zango ya fito daga 2015 zuwa 2019 kuma ya shahara sosai ya samu ƙarɓuwa a gun jama'a. Ma'aikatan Kvartal 95 ne suka ƙirƙiro wata jam'iyyar siyasa mai suna iri ɗaya da sunan gidan talabijin ɗin shi (Shows TV) a watan Maris shekarar 2018.

Zelenskyy ya sanar da maganar tsayawa takararsa a zaɓen shugaban ƙasar Ukraniya na shekara ta 2019 a yammacin ranar 31 ga Disamba shekara ta 2018, tare da jawabin jajibirin sabuwar shekara na shugaban ƙasar Petro Poroshenko akan tashar talabijin ta 1+1 TV channel. Ɓangaren siyasa, ya riga ya zama ɗaya daga cikin masu fafutukar neman shugabanci a siyasance, ya lashe zaɓen ne da kashi 73.2 na ƙuri'un da aka kaɗa a zagaye na biyu, inda ya doke Poroshenk. An gane cewa shine ya shahara sosai a lokacin. ya yima kansa laƙabi da ɗan gwagwarmayar kafa sabbin cigaba (anti-establishment), da kuma wargaje cin hanci da rashawa (anti-corruption).

A matsayinsa na shugaban ƙasa, Zelenskyy ya kasance mai goyon bayan gwamnatin zamani ta e-government da haɗin kai tsakanin sassan ƙasar Ukraniya da masu magana da harshen Rashanci. Salon yadda yake amfani da kafofin watsa labarun yana burgewa sosai, musamman a Instagram .

Gwamnatin Zelenskyy ta fuskanci babban hatsaniya da ƙasar Rasha a cikin shekara ta 2021, wanda a ƙarshe taƙaddamar ta haifar da har sai da shugaban ƙasar Vladimir Putin Rasha ya bada umurnin sojojin Rasha su mamaye ƙasar Ukraniya a watan Fabrairu shekara ta 2022. Dabarar Zelenskyy a lokacin da Rasha ta girke sojojin ta don mamaye Ukraniya ita ce kwantar da hankalin al'ummar Ukraniyawa tare da tabbatar wa ƙasashen duniya cewa Ukraniya ba ta neman daukar fansa akan Rasha. Bayan da Rasha ta fara mamaye Ukraniya, Zelenskyy ya ayyana dokar-ta-ɓaci a duk faɗin ƙasar da taron gama gari.

Manazarta

🔥 Top keywords: