Pele

Edson Arantes do Nascimento (lafazi|ˈɛtsõ (w)ɐˈɾɐ̃tʃiz du nɐsiˈmẽtu; an haifeshi ranar 23 ga watan Octobar, 1940- ya mutu ranar 29 ga watan Disamba 2022) anfi saninsa da Pelé (peˈlɛ) tsohon dan'wasan kwallon kafane na kasar Brazil, wanda yake buga gaba. Wadanda ke wasanni har da marubuta wasan ƙwallon ƙafa, yan wasa, da yan kallo (magoya bayan) na ganinsa a matsayin babban ɗan wasa a duniya. A shekara ta 1999, an zaɓe shi Dan Ƙwallon FIFA na ƙarni na Duniya daga hukumar International Federation of Football History & Statistics (IFFHS) kuma yana daga cikin biyun da aka zaɓa aka ba kyautar ɗan ƙwallon FIFA na ƙarni a wannan shekarar, an zabi Pelé amatsayin ɗan wasan motsa jiki na ƙarni daga hukumar International Olympic Committee. A cewar IFFHS, Pelé shine wanda yafi kowa samun nasarar zura kwallaye a raga a gasar league goal-scorer a tarihin kwallon kafa, inda ya zura kwallaye 650 a wasanni 694, League matches, a kuma gaba daya wasanni da yayi guda 1363 yaci kwallo 1281, har wasannin sada zumunci. Har wayau Pele shine Guinness World Record.[1][2][3][4][5] A lokacin da yake wasannin sa, Pelé shine wanda akafi biya acikin yan'wasa a duniya.

Pele
3. Minister of Sports of Brazil (en) Fassara

1 ga Janairu, 1995 - 31 Disamba 1998
Bernard Rajzman (en) Fassara - Rafael Greca (en) Fassara
Rayuwa
Cikakken sunaEdson Arantes do Nascimento
HaihuwaTrês Corações (en) Fassara, 23 Oktoba 1940
ƙasaBrazil
ƘabilaAfrican Brazilians (en) Fassara
Harshen uwaPortuguese language
MutuwaMorumbi District (en) Fassara da Albert Einstein Israelite Hospital (en) Fassara, 29 Disamba 2022
MakwanciMemorial Necropole Ecumenica (en) Fassara
Yanayin mutuwaSababi na ainihi (Ciwon daji mai launi
multiple organ dysfunction syndrome (en) Fassara)
Ƴan uwa
MahaifiDondinho
Abokiyar zamaAssíria Nascimento (en) Fassara  (30 ga Afirilu, 1994 -  2008)
Marcia Aoki (en) Fassara  (2016 -  2022)
Ma'aurataXuxa
Yara
Karatu
HarsunaPortuguese language
Turanci
Yaren Sifen
Sana'a
Sana'aɗan wasan ƙwallon ƙafa, ɗan siyasa, ɗan wasan kwaikwayo da Jarumi
Hanya
ƘungiyoyiShekaruWasanni da ya/ta bugaƘwallaye
Bauru Atlético Clube (en) Fassara1953-1956
  Santos F.C. (en) Fassara1956-1974659643
  Santos F.C. (en) Fassara1957-19741,1161,091
  Brazil national football team (en) Fassara1957-19719277
New York Cosmos (en) Fassara1975-197765111
 
Muƙami ko ƙwarewaAtaka
Mai buga tsakiya
Lamban wasa10
Nauyi74 kg
Tsayi173 cm
Wurin aikiBrasilia
EmployersMajalisar Ɗinkin Duniya
Kyaututtuka
Sunan mahaifiPelé
IMDbnm0671446
pele10.org
Pele tare da Ben a wani taro
Pele yakai ziyara wata Academy
Pele a wani taro
Pele tare da wani masoyin sa
Pele a Yayin da yake taka leda a 1960
mutum mutumi na Pele
Rubuta sunan Pele
makaranta kenan mai dauke da sunan Pele

Mutuwa

A ranar 21 ga Disamba 2022, Asibitin Albert Einstein, inda ake jinyar Pelé, ya bayyana cewa ciwon kansar sa ya ci gaba kuma yana buƙatar "kulawar gaggawa game koda da zuciyarsa kan rashin aikin (dysfunctions) na ɓangarorin yanda ya kamata".[6] Pelé ya mutu a ranar 29 ga Disamba 2022, yana da shekaru 82 a duniya, sakamakon gazawar gabobi da yawa, mai rikitarwa na kansar hanji.[7][8]

'Yan wasan ƙwallo na duniya sun nuna alhininsu akan tsohon shahararren ɗan kwallon, ciki har da Neymar, Cristiano Ronaldo, Kylian Mbappé da Lionel Messi, da sauran manyan jiga-jigan ƴan wasanni, shahararrun mutane, da shugabannin duniya.[9][10][11][12] Shugaban Brazil, Jair Bolsonaro, ya ayyana zaman makoki na kwanaki uku a ƙasar.[13] An ɗaga tutocin ƙasa na ƙungiyoyi 211 na FIFA a hedkwatar FIFA da ke Zürich.[14] Filayen wasannin an ɗaga tutoci don girmama Pelé cikin filayen da suka daga wannan tuta sun haɗa da; Christ the Redeemer da filin wasa na Maracanã Stadium a birnin Rio de Janeiro,[15] hedkwatar CONMEBOL a Paraguay[13] da filin wasa na Wembley Stadium a London.[16]

Za a yi jana'izar Pelé a filin wasa na Santos a ranakun 2 da 3 ga watan Janairu 2023.[17][18]

Binnewa

Bayan jana'izar, za a binne Pelé a Memorial Necrópole Ecumênica.[19]

Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.


Manazarta

🔥 Top keywords: