Hassan Rouhani
Hassan Rouhani (an haife shi a ranar 12 ga watan Nuwamban shekarar 1948)[1][2] ɗan siyasa ne mai kishin Islama, kuma shugaba na bakwai bayan kaddamar da juyin juya hali na kasar.shugaban kasar Iran ne daga shekara ta 2013 zuwa 2021. Har ila yau, lauyan shari'a ne ("Wakil"), malami[3], tsohon jami'in diflomasiyya kuma malamin addinin Islama. Tun shekarar 1999 Rouhani ya kasance memba a majalisar kwararru ta Iran.[4] Ya kasance memba na Majalisar Expediency daga shekarar 1991 zuwa 2021,[5] kuma ya kasance memba na Majalisar Koli ta Tsaro ta Kasa daga shekarar 1989 zuwa 2021.[6][7] Rouhani ya kasance mataimakin kakakin majalisar dokokin Iran (Majalis) na hudu da na biyar kuma sakataren majalisar koli ta tsaron kasa daga 1989 zuwa 2005.[8] A karshen wannan matsayi, shi ne babban mai shiga tsakani na kasar tare da EU guda uku, Birtaniya, Faransa, da Jamus, kan fasahar nukiliya a Iran, kuma ya yi aiki a matsayin mujtahid na Shi'a (babban malamin addini),[9] kuma mai shiga tsakani kan cinikayyar tattalin arziki.[10][11]
Hassan Rouhani | |||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
3 ga Augusta, 2013 - 3 ga Augusta, 2021 ← Mahmoud Ahmadinejad - Ebrahim Raisi →
3 ga Augusta, 2013 - 17 Satumba 2016 ← Mahmoud Ahmadinejad - Nicolás Maduro (en) →
12 Oktoba 1989 - 15 ga Augusta, 2005
28 Mayu 1984 - 27 Mayu 2000 District: Tehran, Rey, Shemiranat and Eslamshahr (en)
28 Mayu 1980 - 27 Mayu 1984 District: Semnan (en) | |||||||||||
Rayuwa | |||||||||||
Haihuwa | Sorkheh (en) , 12 Nuwamba, 1948 (75 shekaru) | ||||||||||
ƙasa | Iran | ||||||||||
Harshen uwa | Farisawa | ||||||||||
Ƴan uwa | |||||||||||
Mahaifi | Haj Asdollah Fereydoon Rohani | ||||||||||
Abokiyar zama | Sahebeh Rouhani (en) (1972 - | ||||||||||
Yara | |||||||||||
Ahali | Hossein Fereydoun (en) | ||||||||||
Karatu | |||||||||||
Makaranta | Qom Seminary (en) (1961 - 1978) : Fiƙihu University of Tehran (en) (1969 - 1972) Bachelor of Arts (en) Glasgow Caledonian University (en) (1990 - 1995) Master of Philosophy (en) : Doka Glasgow Caledonian University (en) (1995 - 1999) Doctor of Philosophy (en) : constitutional law (en) | ||||||||||
Matakin karatu | doctorate (en) | ||||||||||
Thesis | The flexibility of Shariah (Islamic law) with reference to the Iranian experience | ||||||||||
Harsuna | Farisawa Turanci Larabci Sorkhei (en) | ||||||||||
Sana'a | |||||||||||
Sana'a | ɗan siyasa, Mai wanzar da zaman lafiya, marubuci, Malamin addini da Lauya | ||||||||||
Mahalarcin | |||||||||||
Employers | University of Tehran (en) | ||||||||||
Imani | |||||||||||
Addini | Shi'a | ||||||||||
Jam'iyar siyasa | Moderation and Development Party (en) Islamic Republican Party (en) Combatant Clergy Association (en) | ||||||||||
IMDb | nm3358994 | ||||||||||
president.ir | |||||||||||
A ranar 7 ga watan Mayun 2013, Rouhani ya yi rajista don zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 14 ga watan Yunin 2013.[12] Ya ce, idan aka zabe shi, zai shirya “yarjejeniya ta kare hakkin jama’a”, da maido da tattalin arzikin kasar, da kyautata alaka mai tsami da kasashen yammacin duniya[13]. Ya kuma bayyana goyon bayansa a hukumance domin kare hakkin kananan kabilu da na addini.[14] An zabe shi a matsayin shugaban kasar Iran a ranar 15 ga watan Yuni, inda ya doke magajin garin Tehran Mohammad Bagher Ghalibaf da wasu 'yan takara hudu.[15][16][17]Ya fara aiki a ranar 3 ga Agusta 2013.[18]. A cikin 2013, mujallar Time ta sanya shi cikin jerin mutane 100 da sukafi tasiri a duniya.
Farkon Rayuwa da Ilimi
An haifi Hassan Rauhani a ranar 12 ga watan Nuwamban 1948[19] a birnin Sorkheh, dake kusa da Sorkheh,